• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, April 5, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Kidinafas sun sace mahaifiyar Rarara

by ALI KANO
June 28, 2024
in Labarai
0
Kidinafas sun sace mahaifiyar Rarara

Dauda Rarara da mahaifiyar sa Hajiya Halima

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ƁARAYI masu garkuwa da mutane, wato ‘yan kidinafin, sun sace Hajiya Halima Adamu, mahaifiyar fitaccen mawaƙi Dauda Abdullahi Kahutu (Rarara).

Majiyar mujallar Fim ta ce sun ɗauke ta ne a gidan su da ke garin Kahutu a Ƙaramar Hukumar Ɗanja da ke cikin Jihar Katsina.

Majiyar ta ƙara da cewa ɓarayin sun kutsa kai cikin gidan da misalin ƙarfe 1 na daren jiya, su ka yi awon gaba da dattijuwar.

Majiyar ta ce: “Ɓarayin sun zo ne a ƙafa ba tare da wata hayaniya ba, domin kuwa ba su yi harbi ko ɗaya ba, kuma su ka gama komai cikin mintina ƙalilan. Tsohuwar ba ta yi wata gardama ba lokacin da su ka ce mata ta tashi su tafi.

“Duk da yake ɓarayin sun samu wasu mutanen a gidan, sai su ka ɗauki mahaifiyar Rarara ita kaɗai.

“Ba a yi ƙoƙarin tare su a gidan ba saboda su na ɗauke da bindigogi.

“Watakila sun ɓoye baburan su a nesa sannan su ka taka da ƙafa zuwa cikin gari.

“Mu na addu’ar za a dawo mana da ita lafiya ƙalau domin ta na taimakon mu sosai a garin nan.

“Ɗan ta Rarara ma ya na taimaka mana ƙwarai da gaske. Ya kawo cigaba mai yawa a nan garin don jin daɗin mu.”

Mujallar Fim ta yi ƙoƙarin jin ta bakin Rarara amma hakan bai samu ba saboda layin wayar sa na kashe.

Loading

Tags: barayinDauda Abdullahi Kahutu RararaKahutu
Previous Post

Ibrahim Yala: Duk cikin mata na uku babu mai haƙurin uwargida ta Nafisa

Next Post

Darakta Hassan Giggs da Muhibbat sun cika shekaru 16 da aure

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
Darakta Hassan Giggs da Muhibbat sun cika shekaru 16 da aure

Darakta Hassan Giggs da Muhibbat sun cika shekaru 16 da aure

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!