ƘASASHE takwas ne, ciki har da Nijeriya, za su fafata a gasar baje-kolin finafinan harsunan Afrika ta Kano, wato ‘Kano Indigenous Languages of Africa Film Market and Festival’ (KILAF), ta bana.
An samu sama da finafinai 65 da su ka shiga gasar, waɗanda a cikin su an samu bakwai daga ƙasar waje.
Shugaban kwamitin gudanarwa na gasar, wadda ake shiryawa a duk shekara, Malam Abdulkareem Muhammad, shi ne ya faɗa wa mujallar Fim haka a lokacin da ya ke ƙarin bayani kan cikar wa’adin da aka ɗauka na shiga gasar.
Wa’adin dai ya cika ne a ranar Juma’a, 14 ga Oktoba, wanda ya sa duk wanda bai shiga ba daga ranar, to lokaci ya ƙure masa, sai dai ya jira shekara mai zuwa.
Abdulkareem ya ce, “Da man mun shirya za a rufe karɓar finafinan ne a ranar 14 ga wata, kuma alhamdu lillah ranar ta zo. An samu nasarori sosai wajen shigar da finafinai fiye da shekarun baya.”
Ya ƙara da cewa: “A baya finafinan da mu ke samu ba su da yawa, musamman daga ƙasashen waje, amma a wannan shekarar mun samu finafinai da su ka shiga daga ƙasashe bakwai kuma da yaruka daban-daban na Afirka.”
Da ya ke magana kan yawan finafinan da su ka shiga, Abdulkareem ya ce, “Finafinan da su ka shiga gasar za su kai 65 ko ma dai su wuce haka, don haka ne ma na faɗa maka gasar wannan shekarar ta fi ta baya.”

Ya ce za a yi tsare-tsaren da aka saba yi, kamar haska fim a sinima da za a yi a Ado Bayero Mall da bikin nuna al’adun Afirka.
Bugu da ƙari, shugaban ya bayyana cewa a bana sun gayyato ministan al’adu na ƙasar Nijar kuma ya amsa masu da cewar zai halarci bikin.
“Mu na fatan samun haɗin kai na masu kishin yaruka da kuma al’adun ƙasashen mu na Afrika,” inji shi.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa an tsayar da ranakun 22 zuwa 27 ga Nuwamba na taron, kuma ranar 26 ne za a yi gagarumin taron karramawa.
Wannan taron na bana dai shi ne karo na biyar da za a yi daga lokacin da aka fara shi.