• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 26, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Dillalan waƙa ne ke kassara mawaƙa – Albashir Hamza Yarima

by DAGA ABBA MUHAMMAD
October 17, 2022
in Mawaƙa
0
Albashir Hamza Yareema

Albashir Hamza Yareema

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

FASIHIN mawaƙin Kannywood, Albashir Hamza Yareema, ya yi kira ga dillalan waƙa da su rage zaluntar mawaƙa da su ke yi.

A hirar sa da mujallar Fim, Albashir, wanda mazaunin Kaduna ne, ya ce babu wata riba da mawaƙi ya ke samu a wurin dillalan waƙa.

Ya ce: “Abin da ya sa na ce haka, faɗuwar da ke cikin hulɗa da dillalan waƙa ta fi ribar da ake samu. Dalilin da ya sa na ce haka kuwa, na farko, babu wani natija da za ka samu a wurin wanda ka yi wa waƙa, na biyu babu wata natija da za ka samu daga wurin waɗanda su ka kai waƙar. 

“Duk mawaƙin da ke waƙa fatan sa ya yi suna, duniya ta san shi. To idan har ya na irin wannan ɗora waƙar, idan ba Allah ya taimake shi ba, ba zai yi sunan ba, sannan ba zai samu kuɗin ba ma da har zai gudanar da rayuwar sa a cikin walwala, saboda bai samu damar ganawa da wanda ya yi wa waƙar ba domin ba shi ba ne ya je a matsayin mawaƙin. Ba a ma san shi ba, kawai shi ribar sa ya yi waƙa, ƙwaƙwalwar shi ta ƙara gogewa. Wannan ita ce kawai ribar.”

Da wakilin mu ya ce masa an ce kuɗi su ke biyan su kafin su yi masu waƙar, sai Yareema ya amsa da cewa, “Na ji daɗin wannan tambayar, gaskiya. Zan yi maka sharhi kaɗan, amma bari in ba ka amsa kafin sharhin. 

“Magana ta gaskiya, ba su biya. Ni dai a irin yadda na rayu har na taso ba biya su ke yi ba, saboda ni yadda na ɗauki waƙa ƙauna ce ke sa ka yi wa mutum; idan ka na ƙaunar mutum za ka yi masa ko kuma jarumta, ai jarumta ke sawa ka ji ka ƙaunaci mutum.

“To, ka yi masa waƙa, amma ba a matsayin kai ba. Abin da dillalan waƙa ke zuwa da shi shi ne, wane don Allah ina so ka yi min waƙa, me zan ba da? Na ɗauki waƙa sana’a, sannan kuma mutuntawa. Wani zai ba ka dubu ɗaya, wani biyu, wani uku, wani zai ba ka mota, wani zai ba ka umara, wani zai ba ka gida. Yanayin yadda zai ƙaunaci waƙar ka da rabon ka, yanayin yadda zai ba ka. Amma su kuma da ya ke dillalai ne, ‘yan kasuwa ne, ni ba na shiryawa da su, saboda na san wata rana za a kai inda zan amfana da wannan waƙar.

“Domin in samu damar amfana da waƙa ta, ba na ciniki da mutum, sai dai in ce masa me ka ke da shi ka ba ni in taimaka maka in yi maka waƙa? A haka mu ke tafiya. 

“Wani zai iya ba ka N10,000, wani da mutunci tsakanin ku, kai za ka cika ka biya kuɗin situdiyo ka yi, wataƙila za a zo maka da romon baka: ‘Ka yi, idan mu ka kai za mu samu alkhairi!’ 

“Inda matsalar ta ke, ba lallai ba ne idan ya samo alkhairin kai ka sani, domin ba lallai ba ne ya ƙara dawowa. Idan ya samu kuma ya na iya komawa wurin wanda ya fi ka suna a harkar. Saboda ai yanzu ya na da kuɗi a hannun sa, to zai iya sawa a yi masa a can ɗin, bayan kuma ya san wancan alkhairin da ya samu ba nashi ba ne shi kaɗai, naku ne, kuma kai ne sila. 

“Sai kuma sharhi da na ce zan yi maka. Shi ɗan kasuwa ne, ya san cewa waƙa ita ce hanya mafi sauƙi da zai iya haɗuwa da ɗan siyasa, babban ma’aikacin gwamnati, ɗan kasuwa da sauran su. Shi ya na da nashi kasuwancin, ta yiwu ya na so ya shigar masa da wani kasuwancin sa; idan ɗan siyasa ne, ya na so ya yi masa riguna ko kuma wasu abubuwa daban, amma kuma ba shi da hanya sai ta hanyar waƙa. Idan ya je da waƙa sai kuma ya samu damar shigar da kasuwancin sa. Daga lokacin shi kuma wanda aka yi wa waƙar sai ya ɗauka shi ɗin ne ya yi, bayan shi kuma sila ya ke nema. 

“Don haka ka ga tun daga nan an manta da kai, ba ka samu komai ba, kai da ka zama sila ɗin. To ka ga kenan faɗuwar ta fi ribar!”

Shin, su mawaƙan ba su yin tsarin da idan su ka yi ciniki da mutum ya biya su kuɗin aikin su da yawa, duk abin da ya je ya samo babu ruwan su da shi? 

Sai Albashir ya amsa da cewa: “Ni saboda na san cewa na ɗauke ta sana’a, sannan Allah (s.w.t.) da kan shi ya ke cewa, ‘Wa man nutalhikimata faƙarnutiya khairan kasir’ – idan Allah ya yi maka hikima tabbas ya yi maka alkhairi mai yawa.

Ban san wani alkhairi nawa ba sama da wannan waƙar, shi ya sa ni ba na yin wannan. 

“Ka ga kenan ba sayar wa da mutum na ke yi ba.”

Albashir Hamza Yarima ya yi wani jan hankali ga dillalan waƙa, imda ya ce, “Ina so in ƙara fahimtar da su cewa su rage zaluntar mawaƙan da su ke yi, domin wannan zalunci ne, ka san kuma Allah ya na yaƙi da mai zalunci. Allah ya ba su dama a yanzu a masana’antar nan, idan ma ba ka yi mu’amala da su ba, ba lallai ka samu abin da ka ke buƙata ba. To su yi amfani da wannan damar da Allah ya ba su domin su taimaki su waɗannan mawaƙan. Jan hankalin da zan yi kenan a gare su, Allah ya sa kuma sun ji.”

Dillalan waƙa dai asalin su ba mawaƙa ba ne, ba su da dangantaka da waƙa. Su dai kawai su na zuwa ne su sa a yi masu waƙa su kai wa wanda su ka sa ka yi wa da sunan su su ka yi waƙar.

Wasu kuma daga nan su ke zama jaruman waƙa. Jaruman waƙa kuma su ne masu sayen waƙa a wurin mawaƙa ko su ba da kuɗi a yi masu, sai su kuma su yi bidiyon ta.

Wasu na ganin irin wannan ne ya kashe mawaƙa da dama a harkar waƙa, domin wasu ke amfana da su. Misali, kamar mawaƙi Sani Liya-liya, sai daga baya mutane su ka san shi, amma da farko duk an ɗauka Yamu Baba shi ne Liya-liya domin kusan dukkan waƙoƙin sa da su ka yi tashe Yamu Baba ne ya hau su a bidiyo.

Ganin mutane Yamu Baba su ka sani, sai shi ma Liya-liyan ya fara fitowa a bidiyo.

Loading

Tags: Albashir Hamza YareemadillalaimawaƙaSani Liya-LiyasiyasawaƙaYamu Babazaluncizamba
Previous Post

KILAF 2022: Ƙasashe takwas za su kara a gasar finafinan Afrika a Kano

Next Post

Rasuwar mahaifiya: Na yi rashin babbar mai mini addu’a – Tijjani Faraga

Related Posts

Za a gabatar da littafin waƙoƙin Salma ɗiyar marubuciya Halima K Mashi ran Asabar
Mawaƙa

Za a gabatar da littafin waƙoƙin Salma ɗiyar marubuciya Halima K Mashi ran Asabar

August 23, 2026
‘Ya’ya biyu mata na Mudassir Kasim sun yi saukar karatun Alƙur’ani
Mawaƙa

‘Ya’ya biyu mata na Mudassir Kasim sun yi saukar karatun Alƙur’ani

August 2, 2026
Sani Danja: Waƙar ‘Barau Jigijim’ ta tayar da ƙura, ya ƙaddamar da gasa a kan ta
Mawaƙa

Sani Danja: Waƙar ‘Barau Jigijim’ ta tayar da ƙura, ya ƙaddamar da gasa a kan ta

July 15, 2026
Za a yi bikin naɗa Rarara Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa a Daura ranar Asabar
Mawaƙa

Za a yi bikin naɗa Rarara Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa a Daura ranar Asabar

December 11, 2025
Hotunan Ranar Farko ta taron tunawa da Makaɗa Kassu Zurmi
Mawaƙa

Hotunan Ranar Farko ta taron tunawa da Makaɗa Kassu Zurmi

April 19, 2025
Abin da ya sa nake rubuta littafin rayuwa ta – Ala
Mawaƙa

Abin da ya sa nake rubuta littafin rayuwa ta – Ala

October 28, 2024
Next Post
Marigayiya Hajiya A'ishatu Usman da Malam Tijjani Faraga

Rasuwar mahaifiya: Na yi rashin babbar mai mini addu'a - Tijjani Faraga

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!