• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, October 11, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Kiran Minista ga ‘yan Nijeriya: Mu dawo da kyawawan ɗabi’un da muka rasa

by WAKILIN MU
April 11, 2024
in Nijeriya
0
Kiran Minista ga ‘yan Nijeriya: Mu dawo da kyawawan ɗabi’un da muka rasa

Alhaji Mohammed Idris (na 2 daga dama) tare da sauran Musulmi suna sallar Idi a Kaduna

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAN Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su dawo da kyawawan ɗabi’un da suka rasa tare da ci gaba da addu’o’in samun zaman lafiya da cigaban shugabannin mu da ƙasar mu.

Ya yi wannan kiran ne a Kaduna bayan kammala Sallar Idi.

An gudanar da sallar ne a makarantar Kaduna Capital da ke Kaduna a ranar Laraba.

Ministan ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu addu’a, tare da amincewa da ƙoƙarin da yake yi na mayar da Nijeriya cikin ƙasashe mafiya inganci a duniya.

Ya ce: “Ana farfaɗo da tattalin arzikin mu, kasuwar canjin kuɗaɗen waje na daidaituwa, ana kuma farfaɗo da harkar noma ta yadda za a samu wadatar abinci ga jama’ar mu. Haƙiƙa yanayin tsaron ƙasar nan ma yana inganta.”

Idris ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi Allah wadai da duk wasu munanan ayyuka da ‘yan ta’adda ke aikatawa, tare da fatan za su tabbatar da cewa ‘yan Nijeriya sun zauna lafiya.

Haka kuma ya bayyana damuwar sa kan yadda a hankali ɗabi’un ‘yan Nijeriya ke taɓarɓarewa tsawon shekaru.

Ya yi kira ga dukkanin mu da mu haɗa kai mu dawo da waɗannan ɗabi’u domin farfaɗo da kan mu da ƙasar mu.

Ya kuma buƙaci matasa da su koyi darasi daga abubuwan da suka faru da dattawan su, kuma su guji biye wa sababbin yayi da duniya ke ciki.

“Nijeriya babbar ƙasa ce; Abin da ya kamata mu yi shi ne mu haɗa kai mu tabbatar an rungumi dukkan kyawawan ɗabi’u domin amfanin Nijeriya,” inji shi.

Ministan ya ƙara da cewa: “Domin Nijeriya ta sake zama babbar ƙasa, dole ne mu canza ɗabi’un mu kuma mu ci gaba da nuna duk wasu ɗabi’u da muka koya a cikin watan Ramadan.”

Minista Idris a masallacin Idi

Babban limamin masallacin Makarantar Capital, Imam Abdurrahman, wanda ya jagoranci sallar, ya gabatar da huɗuba, inda ya yi kira ga Musulmi da Kiristoci da su tabbatar da cewa Nijeriya ta zauna lafiya da haɗin kai.

Shi ma ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su dawo da waɗancan ɗabi’u domin su farfaɗo da ƙasar mu.

Loading

Tags: Alhaji Mohammed Idris MalagiBola Ahmed Tinubuɗabi'u
Previous Post

Saratu Giɗaɗo Musulma ce mai kishin ƙasa, inji A’isha Buhari

Next Post

Ƙungiyar matasa da mata za ta naɗa Ado Gidan Dabino Sarkin Mawallafan Arewa

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Ƙungiyar matasa da mata za ta naɗa Ado Gidan Dabino Sarkin Mawallafan Arewa

Ƙungiyar matasa da mata za ta naɗa Ado Gidan Dabino Sarkin Mawallafan Arewa

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!