WATA ƙungiya mai zaman kan ta, mai suna Arewa Youth and Women for Change (wato Ƙungiyar Kawo Sauyi ta Matasa Da Mata a Arewa), za ta naɗa Malam Ado Ahmad Gidan Dabino matsayin Sarkin Mawallafan Arewa na Farko kuma Jakaden Wanzar Da Zaman Lafiya a Arewa.
Ƙungiyar ta sanar da shi wannan cigaba ne a cikin wata takarda da ta rubuta masa mai kwanan wata 1 ga Afrilu, 2024, wadda ya turo wa mujallar Fim da kwafen ta.
A takardar, mai ɗauke da sa-hannun Sakatare-Janar ta Ƙasa ta ƙungiyar, Jakadiya Sadiya Ahmed Birniwa, sun faɗa masa da Turanci cewa: “Ganin gagarumin ƙoƙarin da ka ke bayarwa wajen inganta rayuwar ɗimbin jama’ar mu, musamman ma dai mata da matasa, Babban Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa na Ƙungiyar Kawo Sauyi ta Matasa Da Mata a Arewa ya yanke shawarar karrama ka saboda wannan ƙoƙari da ka ke yi ta hanyar naɗa ka Sarkin Mawallafan Arewa na Farko kuma Jakaden Wanzar da Zaman Lafiya a Arewa.
“An amince da wannan naɗin ne bayan an yi zurfin nazarin manyan mutane masu yawa.
“Za a yi naɗin ne a wajen bikin karramawa da za a shirya a Gandun Namun Daji na Yankari da ke Bauchi a Bikin Al’adun Borno na Duniya na 2024. Za a sanar da kai duk wasu shirye-shirye da za a yi.”

Jakadiya Sadiya ta taya Malam Ado murnar wannan babban cigaba da ya samu tare da yi masa fatan alheri kan dukkan abubuwan da ya saka a gaba a rayuwar sa.
A ƙarshe ta buƙace shi da ya ba da amsa a rubuce idan ya amince da wannan naɗi da za a yi masa.
![]()







