
ƘUNGIYAR Kannywood Family da ke da guruf a WhatsApp ta yi tankaɗe da rairaya a cikin guruf ɗin nata.
Yau kimanin mako ɗaya kenan da shugabannin ƙungiyar, waɗanda su ka haɗa da tsohuwar jarumar Kannywood, Hajiya Hindatu Bashir, mawaƙi Mudassir Ƙasim, tsohuwar jaruma Wasila Isma’il, Ghali DZ, Ali Rabi’u Ali, da Teema Yola, sun ba da umarnin cewa duk wanda ke cikin guruf ɗin ya gabatar da kan sa.
Hakan ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafe da membobin guruf ɗin su ka riƙa yi kan cewa akwai ‘yan damfara a guruf ɗin masu ƙwace wa mutane shafin su na WhatsApp, sannan su riƙa bi su na tura wa mutane saƙo da cewa mai wannan lambar ya na neman taimakon kuɗi naira kaza, sannan su tura wata lambar asusun banki da wani suna na daban wanda ba na mai lambar WhatsApp ɗin da mutum ya sani ba.
Sannan tun kafin wannan lokacin akwai waɗanda su ka yi ƙorafin cewa akwai ‘yan TikTok a cikin guruf ɗin, wanda kuma guruf na ‘yan fim ne zalla.
Wannan dalili ya sa shugabannin guruf ɗin su ka yanke shawarar kowa ya gabatar da kan sa, inda za ka faɗi cikakken sunan ka, jihar ka, kamfanin da ka ke a Kannywood, aikin ka a masana’antar, garanton ka da kuma hoton ka.
A ranar da aka saka dokar, an ba da kwana uku ne kowa ya gabatar da kan sa, in kuma mutum ya wuce kwana uku, za a cire shi daga guruf ɗin.
Bayan nan an ƙara kwanaki, wanda a daren Lahadi da misalin ƙarfe 12:00 na dare aka rufe guruf ɗin ta yadda babu wanda zai iya tura saƙo, sannan aka fara cire waɗanda ba su gabatar da kan su ba.
Tun farko, Wasila Isma’il ce ta ɗauki ragamar ɗaukar sunayen dukkan waɗanda su ka gabatar da kan su a guruf ɗin, kuma ita ce wadda ta yi aikin cire waɗanda su ka gaza gabatar da kan su.
Kafin ta fara aikin cire mutanen, Wasila ta ce, “Alhamdu lillah, Alhamdu lillah, Alhamdu lillah. Godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki da ya ba ni ikon sauke nauyin alƙawarin da na ɗauka. Mu na matuƙar godiya da haɗin kan ku. Allah ta’ala ya bar ƙauna da zumunci mai ɗorewa, amin ya rabbi.”
Haka ita ma Hajiya Hannatu Bashir ta ce, “Assalamu alaikum. Kyawawan matan Kannywood da kuma kyawawan mazan Kannywood. Ina mana barka da dare. A madadi na da ‘admins’ na wannan gidan ina muku godiya da samun lokaci na ‘introduction’.
“Lailai wannan ya nuna cewa za a yi tafiya mai tsafta da mutunta juna da karamci da amfanar da al’umma da irin baiwar da Allah ya yi mana. Alhamdu lillah, alhamdu lillah.
“Ina ganin mun samu ‘introductions’ na mutane 245. Alhamdu lilah, ina fatan yadda mu ka haɗu a nan gidan Allah ya sada mu a Aljannatul Firdausi baki ɗaya.
“Daɗin daɗawa, gidan ba na mu ba ne mu kaɗai, namu ne baki ɗayan mu, in-sha Allah za mu yi tafiya mai kyau idan har mu ka riƙe wannan zumunci da amanar juna. Allah ya kaɗe mana sharrin shaiɗan. Mu na roƙon Allah ya sa zumuncin nan ya ɗore har zuri’ar mu, amin ya Allah.”
Daga nan kuma sai Wasila ta ci gaba da cire mutanen da ba su gabatar da kan su ba.
Kannywood Family guruf ne wanda aka ƙirƙire shi bayan naɗa Ali Nuhu a matsayin Shugaban Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya (NFC).
Da farko an ƙirƙiri guruf ɗin ne musamman don shirya bikin taya Ali murnar samun muƙamin, wanda aka yi a Kano a ‘yan watannin baya.
Daga baya, sai aka mayar da guruf ɗin na ‘yan Kannywood baki ɗaya, aka sanya masa suna ‘Kannywood Family’.
A kwanan baya, ‘yan guruf ɗin sun haɗa kuɗi, inda su ka ba wasu daga cikin membobin su gudunmawar aure da su ka yi da kuma waɗanda ba su da lafiya.
Guruf ɗin ya haɗa da daraktoci, furodusoshi, jarumai da duk wani mai ruwa da tsaki a Kannywood.
A halin yanzu akwai membobi 320 a cikin guruf ɗin.
![]()







