KWAMISHINAN Shari’a na Jihar Kano, Barista Haruna Isah Dederi, ya sulhunta wani saɓani tsakanin Kwamishinar Raya Al’adu da Yawon Buɗe Ido ta jihar, Hajiya Ladidi Garko, da Manajan Daraktan Hukumar Kula da Masu Yawon Buɗe Ido, Alhaji Tukur Bala Sagagi, tare da Shugaban Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta jihar, Alhaji Abba El-Mustapha.
An yi taron sasantawar a babban ɗakin taro na Ma’aikatar Shari’a a Kano.
Haka kuma, an shirya taron ne domin nemo bakin zaren rashin fahimtar da ke faruwa wajen gudanar da ayyukan da ya rataya a tsakanin hukumomin biyu a kan masu sana’ar gidajen kallo (viewing centres) da masu gidajen shirya tarurruka (event centres).
Da farko Dederi ya yi dogon jawabi dangane da haƙƙi tare da ayyukan da su ka rataya a kan hukumomin biyu, inda bayan doguwar tattaunawa tsakanin shugabannin hukumomin biyu aka samu daidaito.

El-Mustapha ya ba da shawarar a raba ayyukan gida biyu, inda kowace hukuma za ta ɗauki ɗaya don ta mai da hankali a kan sa, ita kuma Hajiya Ladidi ta yi na’am da wannan shawarar.
Bisa la’akari da hakan, sai Dederi ya tabbatar da ba wa kowace hukuma aiki ɗaya don ta mai da hankali a kai don cimma nasarar da gwamnati ta sa a gaba.
A yanzu dai Hukumar Tace Finafinan da Ɗab’i ce ke da alhakin kula da ayyukan masu sana’ar gidajen kallo, ita kuma Hukumar Kula da Al’adu da Masu Yawon Buɗe Ido ke da alhakin kula da ayyukan masu gidajen shirya tarurruka.

Shugabannin sun nuna farin cikin su dangane da yadda Ma’aikatar Shari’a ta kawo ƙarshen taƙaddamar tare da samun nasarar da taron ya samu na cimma matsaya.