Tun da safiyar ranar Litinin ɗin nan, 8 ga Agusta, 2022 aka tashi da labarin wai tsohon jarumin fim Malam Kabiru Nakwango ya rasu. A cikin ɗan lokaci kaɗan labarin ya bazu a soshiyal midiya kamar wutar daji.
Abin sai ya yi kamar ya lafa sai a ƙara bijiro da shi, don haka labarin ya ci gaba da yaɗuwa tsawon wuni guda. Hakan ya sa jama’a su ka kasa gane tantance gaskiyar maganar.
Ko mu ma a mujallar Fim mun yi ta buga wayar jarumin, wani ya na ɗagawa ya na cewa labarin ba gaskiya ba ne domin shi Nakwango ya na gona ya na aiki, shi ya sa ya kasa gamsar da mu.
Sai dai bayan sallar magariba wakilin mu ya je gidan sa da ke unguwar Gwammaja cikin birnin Kano domin tabbatar da labarin. Mun yi sa’a a daidai lokacin ya dawo daga gona, ko fitowa bai yi daga cikin motar sa ba.
FIM: An wayi gari da labarin ƙarya cewa wai ka mutu. Ya ka ji da ka samu wannan mugun labarin?
KABIRU NAKWANGO: To, ni Kabiru Abubakar Aliyu, wanda aka fi sani na da Kabiru Nakwango, ni dai abin da zan ce a game da wannan labarin sai dai na ce Allah ya sauwaƙe, domin ina nan lafiya, Allah ya raya ni har zuwa wannan lokaci da mu ke magana da kai, kuma babu abin da ya same ni.
Kuma yanzu da daddaren daga gona na ke, dawowa ta kenan, ko gida ban shiga ba, don haka ina nan da rai na.
FIM: Ko ya aka yi ka samu wannan labarin?
NAKWANGO: To, ni ban karanta labarin ba, kuma ban samu labarin ba, sai dai mutane da su ka karanta su su ka kira ni su ka faɗa mini. Kuma na amsa kiran waya a yau daga safe zuwa yanzu ya fi ɗari biyar. Kuma aboki na Malam Garba shi ya riƙe wayoyin. Duk wayoyi na guda biyu sai da cajin su ya ƙare saboda kira; ɗayar da ta ke hannu na ita ce ta rage mai caji, kuma ba ta taɓa minti ɗaya ba a kira ba. Saboda haka kira ake ta yi ana tambaya ana jajantawa, ina sanar da mutane cewar ba gaskiya ba ne. Hakan sai ya zamana aikin da zan yi a gona kusan kaso biyu daga cikin uku bai samu ba, saboda mutane su na ta kira su na tambaya.
FIM: Wannan ba shi ba ne karo na farko, a baya ma an taɓa yaɗa irin wannan labarin. To ko ya ka ɗauki wannan lamarin?
NAKWANGO: To, ni dai ga shi lafiya ta ƙalau, babu wata rashin lafiya da na yi. To amma dai abin da zan faɗa wa mutane shi ne yin hakan babu alheri. Domin ka ce mutum ya mutu ba shi zai ƙara masa kwana ba, kuma ba shi zai rage masa kwana ba, kuma ba shi da alaƙa da mutuncin sa ko karamcin sa, ko ɗaukakar sa ko durƙushewar sa. Muhimmin abu shi ne kai da ka rubuta kuma ba haka ba ne, ka ɗaukar wa kan ka wani zunubi, domin duk mai son sa idan ya ji sai hankalin sa ya tashi. Don haka kuskure ne. Kuma mutuwa duk in da ka gan ta, abin da za a yi ne aka yi. Saboda haka babu wani abu na mamaki don kare ya yi haushi. Mutuwa abin da za a yi ne aka yi. To an yi, don haka idan ta zo kan Nakwango zai mutu.
FIM: Ko dai don daɗewar da aka yi ba a ganin ka a fim ne ta jawo wannan ji-ta-ji-tar?
NAKWANGO: Ai kafin na fara fim an san ni a wurare daban-daban. Su da su ka daina gani na a wancan wuraren ya su ka yi? Kuma waɗanda su ka daina gani na a fim ya su ka yi? Ba cewa aka yi Nakwango ya daina yin fim ba, kuma ba cewa aka yi Nakwango ba zai yi fim ba, ko wani ne ya hana shi.
Wannan ba wani abu ba ne, a karan kai na ne na ji gara na ke ɗan hutawa domin babu dalilin da zai sa ka yi ta danna abu a kan ka, ka yi ta yi babu ji ba gani. Ina ɗan hutawa; zuwa wani lokaci za ka gan ni jefi-jefi na fito don mutane su gane ina nan da raina kuma ina yin harkar. Ina roƙon Allah ya taimake mu a kan lamuran mu.
FIM: To madalla, mun gode.
NAKWANGO: Ni ma na gode sosai.
Allah ya raya mana kae
Jarumi kabiru na kwango