• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, April 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Lauyoyi a Kano sun kai kukan su ga sarakunan Jihar Katsina kan ‘waƙoƙin ɓatanci’ na Rarara

by DAGA ABBA MUHAMMAD
April 18, 2023
in Labarai
0
Dauda Rarara

Dauda Rarara

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

WASU lauyoyi a Kano sun kai ƙarar mawaƙi Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara) wajen Sarkin Katsina da Sarkin Daura bisa zargin da su ke yi masa na cin zarafin wasu shugabannin siyasa na Jihar Kano a cikin waƙoƙin sa. 

Lauyoyin sun roƙi sarakunan da su tsawata masa domin ya tuba kuma ya janye kalaman sa a kan shugabannin tare da neman yafiyar su don a zauna lafiya.

Ɗaya daga cikin lauyoyin, Barista Badamasi Sulaiman Gandu, ya bayyana haka a cikin wata hira da ya yi da gidan rediyon Freedom da ke Kano. 

Ya ce tun da farko sun tura wa mawaƙin wasiƙa da ke ɗauke da jan hankali da kira a gare shi da ya tsaftace siyasar shi da salon waƙar sa kasancewar akwai kurakurai da dama a ciki.

Lauyan ya ci-gaba da cewa sun fahimci cewa kalaman da Rarara ke amfani da su a kan shugabannin Jihar Kano sun fara tasiri musamman wajen ƙoƙarin ɓata kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin Katsinawa da Kanawa.

Barista Gandu ya tabbatar da cewa salon waƙoƙin da mawaƙin ke amfani da su sun saɓa wa dokokin ƙasa, domin su kan kawo tarzoma da fitina.

Ya ce haka kuma, bayan cin karo da dokokin ƙasa, waƙoƙin sun saɓa wa koyarwar addinin Musulunci da al’adun mutanen Jihar Kano.

Sannan lauyan ya ƙara da cewa sun rubuta takarda ɗauke da saƙo ga sarakunan da kuma gwamnatin Jihar Katsina da hukumar tsaro don neman a ja masa kunne a matsayin sa na ɗan asalin Jihar Katsina kuma talakan sarakunan.

A wani ɓangaren kuma, Gandu ya nuna takaici bisa waƙar da Rarara ya fitar bayan zaɓen gwamna a Kano wadda ta yi sanadiyyar jawo cin mutunci ga mahaifiyar mawaƙin da wasu ɓatagari su ka yi. 

Ya yi fatan matakin da su ka ɗauka zai taimaka wajen dakatar da mawaƙin daga sake yin waƙoƙin cin mutunci ga shugabannin siyasa na Kano kamar yadda su ke zargi. 

Wasu daga cikin waɗanda ake zargin mawaƙin ya ci mutuncin su a waƙoƙin sa sun haɗa da tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, tsohon gwamnan Kano kuma tsohon sanata, Rabi’u Musa Kwankwaso, da kuma tsohon gwamnan jihar, Sanata Ibrahim Shekarau.

Loading

Tags: Badamasi Sulaiman GanduDauda RararaFreedom RadioGandujeKwankwasoƙaralauyoyiMuhammadu Sanusi IISarkin DauraSarkin KatsinaShekarauwaƙar siyasaZaɓen 2023
Previous Post

Bikin Sallah: Daso ta raba wa mata 60 kyautar atamfofi

Next Post

Daraktan finafinai a Nijar, Bassirou Garba ya zama baban Iklas

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
Darakta Bassirou Garba Sarkin Fulani da 'yar sa Iklas

Daraktan finafinai a Nijar, Bassirou Garba ya zama baban Iklas

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!