• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, July 21, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Maganin barin giɓi: Buhari ya umarci shugabannin Hukumar Haɓaka Arewa-maso-gabas da su kama aiki

by Daga WAKILIN MU
May 20, 2023
in Nijeriya
0
Sababbin membobin hukumar gudanarwar a cikin Ma'aikatar Harkokin Jinƙai a ranar Juma'a da ta gabata

Sababbin membobin hukumar gudanarwar a cikin Ma'aikatar Harkokin Jinƙai a ranar Juma'a da ta gabata

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SHUGABAN Ƙasa Muhammadu Buhari ya umarci membobin sabuwar hukumar gudanarwa ta Hukumar Haɓaka Arewa-maso-gabas (NEDC) da su kama aikin riƙon ƙwarya ba tare da ɓata lokaci ba don kada a bar wajen babu shugabanni.

Shugabannin za su yi aiki ne kafin su samu tabbacin naɗin su daga Majalisar Dattawa kamar yadda doka ta tanada.

Wata sanarwa ga manema labarai da Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Dakta Nasir Sani-Gwarzo, ya rattaba wa hannu ta ce an yanke wannan shawarar ne don kada a bar wajen babu shugabanni.

Haka kuma shugaban ƙasa ya amince da cewa sabon Manajan Darakta kuma Shugaban hukumar, Alhaji  Umar Abubakar Hashidu, shi ma ya kama aiki a matsayin riƙo kafin ya samu amincewar Majalisar Dattawa. 

Dakta Gwarzo ya ce hakan ta faru ne bayan ƙarewar wa’adin tsohon shugaban hukumar da sauran membobin a ranar 7 ga Mayu, 2023. 

A cewar sa, Buhari ya kuma amince wa Lauya Bukar Baale da ya kama aiki a matsayin ciyaman mai riƙon ƙwarya na hukumar tare da membobi 10 na hukumar gudanarwar. 

Bugu da ƙari, shugaban ya ba da umarni ga jami’in da ke riƙe da ofishin manajan daraktan hukumar a yanzu da miƙa ragamar ga sabon da aka naɗa ba tare da ɓata lokaci ba.

Gwarzo ya ce an ba da wannan umarnin ne domin “a kauce wa samun giɓi a wajen gudanar da ayyukan yau da kullum a wannan hukumar mai matuƙar muhimmanci da tasiri kafin lokacin da Majalisar Dattawa za ta ba su tabbacin naɗin su.”

Ita dai Hukumar Gudanarwar ta NEDC ta ƙunshi membobi kamar haka: Suwaiba Idris Baba, Babbar Daraktar Harkokin Agaji (daga Taraba, Arewa-maso-gabas); Musa Umar Yashi, Babban Daraktan Gudanarwa da Harkar Kuɗi (daga Bauchi, Arewa-maso-gabas); Dakta Isma’ila Nuhu Maksha, Babban Daraktan Gudanarwa (daga Adamawa, Arewa-maso-gabas), da Umar Abubakar Hashidu, Manajan Darakta/Shugaba (daga Gombe, Arewa-maso-gabas).

Sauran su ne Onyeka Gospel-Tony, Memba, (daga Kudu-maso-gabas); Hon. Madam Hailmary Ogolo Aipoh, Memba (daga Kudu-maso-kudu); Eya Kwamanda Babatunde Akanbi (ritaya), Memba (daga Kudu-maso-yamma); Mustapha Ahmed Ibrahim, Memba (daga Arewa-maso-yamma); Hadiza Maina, Memba (daga Arewa-ta-tsakiya), Alhaji Grema Ali, Memba (daga Arewa-maso-gabas), da kuma wakili daga Ma’aikatar Kuɗi, Kasafi da Tsare-tsaren Ƙasa ta Tarayya.

Loading

Previous Post

INEC ta rantsar da Isah matsayin kwamishina a karo na biyu

Next Post

Mawaƙi a Kannywood, Abba Zakin Hausa, ya zama angon Asiya

Related Posts

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim
Nijeriya

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim

July 15, 2025
Nijeriya

Tinubu yana goyon bayan Ƙananan Hukumomi su ci gashin kan su – Minista

July 11, 2025
Nijeriya

Shirin Sabunta Fata na Tinubu yana samar da damarmakin cigaba — Minista

July 10, 2025
Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista
Nijeriya

Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista

July 10, 2025
Ministoci za su fara gabatar da rahoton ayyuka a taron manema labarai
Nijeriya

Tinubu ba zai yarda hayaniyar siyasar 2027 ta ɗauke masa hankali ba – Minista

July 8, 2025
Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano
Nijeriya

Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano

July 8, 2025
Next Post
Abba Zakin Hausa da 'yan'uwan sa jim kaɗan bayan ɗaurin auren a Zariya

Mawaƙi a Kannywood, Abba Zakin Hausa, ya zama angon Asiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!