ALLAH ya yi wa mahaifin jarumar Kannywood, Fati S.U. Garba, rasuwa.
Alhaji Sulaiman, wanda aka fi sani da Dakta S.U. Garba ya rasu ne da misalin ƙarfe 1:30 na ranar Lahadi, 19 ga Maris, 2023 a gidan sa da ke Minna, Jihar Neja, bayan ya yi doguwar jinya.
An yi jana’izar sa da misalin ƙarfe 4:30 na yamma.
Ya rasu ya na da shekara 90 a duniya, kuma ya bar ‘ya’ya 18.
A yau Talata, 21 ga Maris, an yi addu’ar uku a gidan sa.
Fati S.U. Garba ta yi wa mahaifin ta addu’ar samun rahama da kuma saduwa da mala’ikun rahama. Ta kuma ce, “Allah ya sa halin sa nagari ya bi shi domin mutumin kirki ne kuma uba nagari, sannan miji nagari.”
Yanzu dai Fati ta zama marainiya gaba da baya domin a ranar Asabar, 18 ga Satumba, 2021 mahaifiyar ta ta rasu. Tsakanin rasuwar mahaifin ta da ta mahaifiyar ta shekara ɗaya da wata shida da kwana ɗaya.
Allah ya jiƙan su da rahama.