A RANAR Alhamis, 29 ga Maris, 2024 Allah ya azurta matashin makaɗi kuma mawaƙi a Kannywood, Musa Muhammad, wanda aka fi sani da Ahmad Yarima, da ‘ya mace.
Maiɗakin sa, Malama Adama Abubakar, ta haihu da misalin ƙarfe 7:38 na yamma a Babban Asibitin Kawo, Kaduna.
A yau Alhamis, wadda ta kama mako guda kenan da haihuwar, aka raɗa wa jaririyar suna Fateema (Afreen) a masallacin Hai’ah da ke Malalin Gabas, Kaduna.
Haka kuma an yi taron suna a gidan Yarima da ke Malalin Gabas.
Allah ya raya Fateema, ya albarkaci rayuwar ta.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa Yarima ya na daga cikin matasan makaɗa da tauraruwar su ke haskawa a wannan zamani.