ALLAHU Akbar! Allah ya yi wa sananniyar marubuciyar Hausa ɗin nan Hadiza Salisu Sharif rasuwa a yau.
Ta rasu a Kano sakamakon cutar daji (cancer) wadda ta mamaye cikin cikin ta.
Fauziyya D. Sulaiman, marubuciya mai fafutikar nema wa mabuƙata agaji, ita ce ta bayyana labarin rasuwar ɗazu a Facebook.
A saƙon da ta rubuta kan al’amarin, ta ce: “Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un. Ina mai alhinin sanar da ku rasuwar ‘yar’uwar mu Hadiza Salisu Sharif yanzu. Ana ta ƙoƙarin fitar da ita waje, ashe babu rabon ta rayu.
“Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un. Allah ya gafarta wa Hadiza, Allah ya sa bakin wahalar ta kenan, amin Allah.”
Wannan sanarwar ta girgiza mutane da dama a soshiyal midiya inda aka yi caa ana bayyana alhini kan rasuwar, tare da yi wa marigayiyar addu’ar samun rahamar Allah.
Idan kun tuna, mujallar Fim ta ba ku labari a ranar 9 ga Agusta, 2023 yadda Fauziyya D. Sulaiman ta ba da sanarwar nema wa Hadiza agajin gaggawa daga bayin Allah saboda matsanancin rashin lafiyar da ta ke fama da shi.

A saƙon da ta wallafa tare da bidiyo na majinyaciyar a soshiyal midiya a ranar, Fauziyya ta bayyana cewa Hadiza ta kwana biyu ta na jinya a asibitoci daban-daban, ana ta kashe kuɗi masu yawa, amma babu sauƙi.
Ta ce: “Ruwa ne ya ke taruwa a cikin ta. An tattara kuɗi an yi mata aiki, sai dai gurin yin aikin aka gano ‘cancer’ ta mamaye cikin ta gaba ɗaya, inda likitoci su ka tabbatar da sai an fita da ita ƙasar Indiya domin yi mata aiki. Ana neman kuɗin aiki naira miliyan biyar.”
Ta ƙara da cewa: “Mun yi iyakacin yin mu, amma babu yadda za mu yi, dole sai mun fitar da wannan bidiyon domin nema mata taimako a gurin ku al’umma.
“Tabbas kuɗin su na da yawa, amma da kwabo da sisi da taro in-sha Allah za mu haɗa wannan kuɗin jama’a.”
Fauziyya ta yi kira ga jama’a da don Allah su taimaka sannan su taya ta yaɗa bidiyon majinyaciyar da aka yi domin mutane su gani.
Sakamakon wannan yekuwar, mutane sun riƙa tura kuɗi a asusun banki na marigayiyar, inda washegari wani mutum da ba a bayyana ko wanene ba ya tura mata naira miliyan biyar a asusun nata domin nemar mata magani.
A sanarwar da ta bayar kan wannan agajin na miliyan biyar, Fauziyya ta ce: “Wallahi jiki na rawa ya ke saboda farin ciki. Allah ya faranta wa wannan bawan Allah, Allah ya dubi iyalin sa. Mun gode, mun gode, mun gode.”
Allahu Akbar! Ashe ciwon ba na tashi ba ne.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa Hadiza Salisu Sharif ita ce marubuciyar littattafai da su ka haɗa da ‘Sarauniyar Mata’, ‘Salon So’, ‘Gyaran Mace’, ‘Rufaida ko Mufida?’, ”Yanbiyu’, ‘Jarrabar Rayuwa’, ‘Maraicin ‘Ya Mace’, ‘Matar So’, ‘Matar Uba’, ‘Rayuwa Ta’, ‘Sinadarin Masoya ‘, ‘Haka Za Kai Min!’, da kuma ‘Guzirin Zaman Miji’.
Haka kuma ta yi fice wajen taimaka wa ma’aurata da magungunan gyaran aure da kuma shawarwari na zamantakewar gidan miji.
Allah ya jiƙan ta, ya sa ƙarshen wahalar kenan.
Ita ma Fauziyya, ɗimbin mutane na ta yi mata addu’ar Allah ya saka mata da alheri.
![]()







Allah ya jikanta