JARUMI Ali Nuhu ya yi kira ga masoyan sa na soshiyal midiya da su daina zagin mawaƙi Davido saboda cin zarafin Musulunci da ya yi tunda dai ya goge bidiyon daga shafukan sa na soshiyal midiya.
A jiya mujallar Fim ta ba da labarin taƙaddamar da ta ɓarke bayan Davido ya wallafa bidiyon wata waƙa da wani sabon mawaƙi wai shi Logos Olori ya yi inda aka nuno wasu mutane a matsayin Musulmi da su ka fasa sallar da su ke yi a masallaci su ka shiga rawar waƙar tasa.
Davido, wanda shi ne ya ɗauki nauyin shirya waƙar, ya wallafa bidiyon ta a Twitter da Instagram, wanda hakan ya janyo masa tsinuwa da zagi daga ‘yan Kannywood da sauran jama’a a soshiyal midiya, cikin su har da Ali Nuhu.
To amma Ali ya ce a ƙyale shi tunda dai ya goge bidiyon.
A saƙon da ya wallafa a Instagram, jarumin ya gode wa mawaƙin saboda ya ji kiraye-kirayen da aka yi masa har ya ɗauki mataki.
Ya ce da Turanci: “Thank you for deleting that post @davido, to everyone who felt offended by his post please let sleeping dogs lie. Let love lead, I am personally not against anyone but please I am appealing to all my fans to desist from dragging, abuse or insult. Thanks.”
Fassarar rubutun nasa ita ce: “Ina gode maka da ka goge saƙon nan, Davido. Ga duk wanda ya ji zafin saƙon da ya tura kuwa, don Allah a bar maganar ta wuce. Mu bari soyayya ta fi komai. Ni a kankin kai na ba na adawa da matsayin kowa, amma ina kira ga dukkan masoya na da su daina jan maganar ko zagi ko cin mutunci. Na gode.”
Mutane da dama sun goyi bayan abin da Ali ya faɗa, amma wasu kuma sun ce ba haka ba ne.
Jarumi kuma furodusa Jamilu Yakasai (‘Dakanɗaka’) ya faɗa wa Ali Nuhu cewa wannan saƙo nasa abin kunya ne.
Jamilu, wanda abokin Alin ne, ya ce masa da Turanci: “This is a shame, posting Davido picture and thanking him at the moment because he is not the one (who) removed the post, the post was removed by Instagram and even (if) he is the one (who) removed (it) he (does) not deserve this post @realalinuhu.”
Fassarar saƙon shi ne: “Wannan abin kunya ne da ka wallafa hoton Davido har ka na gode masa a yanzu, domin ai ba shi ba ne ya goge saƙon, Instagram ne su ka cire shi, kuma ko da shi ɗin ne ya goge shi bai cancanci wannan saƙon ba Ali Nuhu.”
Nan take sai Ali ya ba shi amsa da cewa: “Mu fahimci wannan abu da kyau Jamilu, addinin mu bai goyi bayan abin da ka rubuta a nan ba. Wannan ra’ayin ka ne. Ya kamata mu nuna Musulunci da kyau. Wasu mutanen mushrikai ne kafin zuwan annabin mu mai tsarki amma daga baya su ka dawo su ka karɓi Musulunci. Shin an ƙi karɓar su ne? Kuskure na mutum ne amma yafiya ta Allah ce.”
Haka dai aka ci gaba da tataɓurza a shafin Ali Nuhu na Instagram da wasu wuraren kan wannan al’amari.
Mumajin Dadin yadda kuke kawo muna bayanai masu zafi da dumi duminsu a kannywood thank you