SABON Babban Sakataren Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Alhaji Abba El-Mustapha, ya shiga ofis domin kama aiki a yau tare da yin kakkausan gargaɗi ga ɓata-gari da ke shigowa Kannywood don su ɓata al’amurra da su kama gaban su.
Ya ce shi aiki ya zo yi, ba wasa ba.
Shugaban ya faɗi haka ne a yau lokacin da ma’aikatan hukumar da ƙungiyoyin ‘yan fim da kuma ‘yan siyasa su ka yi dafifi a ofishin hukumar da ke Titin Maiduguri a Unguwar Hotoro, Kano, bayan sun yi masa rakiya don ya kama aiki.
A lokacin da ya ke jawabi ga jama’ar da ta taru a wurin, El-Mustapha ya sha alwashin yin duk mai yiwuwa wajen kawo gyara da kyautata ɗabi’un jama’a a matsayin sa na shugaban hukumar a iya tsawon lokacin da Allah ya ba shi.
Ya bayyana cewa akwai wani ciwo da ke damun sa game da industiri, kuma yanzu dama ta samu ta warkar da shi.
El-Mustapha ya ce: “Ni ɗan fim ne; ina matsayin jarumi, marubucin labari, furodusa, kuma wani lokacin na kan zama darakta, don haka akwai wani ciwo da ya ke damu na a zuciya ta tsawon lokaci, wanda duk lokacin da na tuna abin ya kan yi mani ciwo a zuciya.

“Ba ni kaɗai ba, duk wani mai kishin wannan masana’antar ya na da wannan ciwon, kuma wannan ba wani ciwo ba ne sai irin yadda lamurra su ka lalace a wannan masana’antar ta hanyar rashin tsari. Don haka a wannan lokacin mun shirya mu yi gyara.
“Saboda haka duk wanda ya ke gudanar da wasu ayyuka da ba su dace ba, to idan har ba zai daina ba, to ya kama gaban sa, domin ba za mu bari a ci gaba da yin abubuwan da ba su dace ba. Mu masu kishin addinin mu ne da yaren mu da kuma al’adun mu.”
Shugaban ya nemi haɗin kai daga ma’aikatan sa da ‘yan industiri, ya na cewa: “Babban abin da na ke buƙata ga abokan aiki na na wannan gida da kuma abokan sana’a ta ‘yan fim shi ne ina fatan ku ba ni haɗin kai da goyon baya tare da shawarwari masu inganci don ganin mun samu nasarar burin yin aikin da mu ka sa a gaba.
“Kuma ina ƙara tabbatar maku da cewa aiki mu ka zo, ba wasa ba. Duk wanda ya ke ganin zai kawo mana ɓarna a wannan masana’antar, to tun wuri ya kama gaban sa.”
Mujallar Fim ta ruwaito cewa rakiyar da ‘yan fim su ka yi wa El-Mustapha tun daga Zoo Road har zuwa sabon ofis ɗin sa ta nuna kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin sa da ‘yan fim da sauran jama’a, domin kusan duk wani jarumi da ake ji da shi a Kannywood ya halarci wajen.

Kaɗan daga cikin su su ne Ali Nuhu, Baballe Hayatu, Abbas Sadiq, Abubakar Bashir Maishadda, Saratu Giɗaɗo, Asma’u Sani, Isa Bello Ja, Yahanasu Sani, Salisu Officer, Misbahu M. Ahmad, Alhassan Kwalle, Lawan Ahmad, Maryam CTV, Mu’azzam Idi Yari, Alhaji Sheshe, Kabiru Musa Jammaje, da Naziru Ɗanhajiya.



![]()







