AN bayyana haɗin kan ‘yan fim a matsayin wani jigo ga cigaban masana’antar da kuma kuma samun martaba a gare su.
Wannan kalamin ya fito ne daga bakin shugabar ƙungiyar ‘Matan Mu A yau Organisation Kannywood Artists’, Hajiya Zulai Bebeji, a lokacin da ta ke yi wa mujallar Fim bayani a Kano a game da manufofin ƙungiyar.
Ta ce: “Mu dai mata ‘yan fim mun yi ƙoƙarin samar da wannan ƙungiyar ne tun kusan shekaru biyu da su ka wuce inda mu ka yi ta faɗi-tashin ganin ƙungiyar ta zauna da gindin ta don ta zama wata inuwa ta haɗin kai da kuma taimakon juna a tsakanin mu. Kuma alhamdu lillah kamar yadda abubuwa su ke tafiya a yanzu, mun fara ganin hasken tafiyar.”

Ta ci gaba da cewa, “Da farko mun yi tunanin tafiyar da ƙungiyar iyakar mu mu mata, amma daga baya sai mu ka faɗaɗa mu ka shigo da maza saboda duk wata harkar da mata za su yi sai maza sun shigo za a samu abin da ake so na cigaba, don haka ne mu ka shigo da maza a cikin tafiyar, amma dai mata sun fi yawa.”
Da mujallar Fim ta tambaye ta abin da ƙungiyar ta fi mayar da hankali a kan sa kuwa, cewa ta yi, “To, mu na mayar da hankali wajen wayar da kan ‘yan fim wajen kula da muhimmancin sana’ar su don su kare mutuncin su da kuma masana’antar, don haka ne ma mu ke haɗa taruka mu na gayyato manyan mutune su na yi mana jawabi. Sannan mu na kai ziyara ga shugabanni da kuma ‘yan siyasa domin gabatar da kan mu da kuma manufar tafiyar mu. Sannan mu na ƙoƙarin samar wa ƙungiya ayyuka a wajen kamfanoni da kuma ‘yan siyasa.
“Kuma duk wata jaruma da ta ke cikin mu mu na ƙoƙarin samar mata da aiki a wajen manyan furodusoshin mu na Kannywood.”
A game da yadda ake kallon ƙungiyar kamar ta tsofaffin ‘yan fim ce, musamman mata, Hajiya Zulai ta ce: “Ƙungiyar mu ta kowa da kowa ce, yara da manya. Don haka ne ma ake yi wa tafiyar tamu kallon kamar ta manyan ‘yan fim. To mu mu na yi ne da kowa, don ba mu ware ba, kowa ya shigo namu ne, da ɗan wasan daɓe da duk wani wanda ya ke da harkar sana’a a cikin masana’antar fim. Don haka ƙungiyar mu ta kowa ce in dai ya na cikin Kannywood.”
Membobin ƙungiyar dai sun haɗa da Hajiya Zulai Bebeji, Bilki Madaki Maryam Muhammad (Maryam CTV), Hamza Adamu Indabawa, Nura MD, Hajiya Halima Sagir, Ruƙayya Sharaɗa, Zainab Isa Jalingo, Hajiya Maimuna, Hajiya A’isha, Hajiya Sakina, Bilkisu Muhammad, Firdausi KJB, A’isha Muhammad, Aisha KT, Hajiya Hauwa Ja’en, Rahama Mil 9, da sauran su.
![]()






