JARUMAN Kannywood sun bayyana damuwa kan yadda ake ci gaba da amfani da soshiyal midiya ana ɓata masu suna ko a yi zamba-cikin-aminci.
Aƙalla jarumai mata guda uku – Farida Jalal, Hadizan Saima, da Hadiza Gabon – sun fito sun yi bayani kan al’amarin tare da nanata cewa wasu shafukan da ke intanet ba nasu ba ne.
Sun yi barazanar cewa su fa ba za su amince ba, za su ɗauki mataki na shari’a da masu damfara da sunayen su.
Hadiza Muhammad, wadda aka fi sani da Hadizan Saima, ta ce wasu ne su ke yin amfani da sunan ta a Facebook su na saka hotunan da ba su dace ba da sunan cewa ita ce ta ke ɗorawa.
Da mujallar Fim ta nemi ƙarin bayani kan lamarin, sai Hajiya Hadizan Saima ta ce: “Ni ba na yin Facebook amma a ‘yan kwanakin nan sai na ji ana ta kira na a waya ana cewa ina ɗora wasu hotuna da ba su dace ba a Facebook da sunan tallar magani.
“Da na ji abin ya yi yawa sai na duba na ga wasu masu tallar magani ne su ka buɗe su ke saka hotunan su na batsa da sunan tallar magani. To gaskiya wannan abin ya yi mani ciwo, don ni ba ni da shafi a Facebook amma wasu su ke amfani da suna na.”
Ta ƙara da cewa, “Gaskiya wannan cin mutunci ne da ba zan lamunta ba. Don me ya sa su ba za su yi amfani da sunan su ba sai dai su yi amfani da suna na su zubar mini da mutunci? Wannan abu ne da ba zan lamunta ba. Ko dai su daina ko na bi haƙƙi na.”
Fitacciyar jarumar ta shaida wa masoyan ta cewa idan su ka ga irin wannan shafin, to su sani cewa ba nata ba ne, “don ni ba na yin Facebook.”
Ita ma jaruma Farida Jalal, wasu ne su ka buɗe shafi a Facebook da sunan “Sayyada Farida Jalal” kuma su na saka hotunan ta da bayanai da su ke nuna daga wajen ta ne.
Amma ta ce: “Ni sam ba ni da wani shafi a Facebook kuma ban taɓa yi ba. In ban da WhatsApp babu wani abu da na ke yi a dandalin sada zumunta, don haka babu wani shafi da na ke da shi a Facebook mai sunan Farida Jalal.
“Abu ɗaya da na sani, akwai Umar Nagudu da ya ke amfani da hotuna na a shafin sa ya na tallar kayayyaki, amma shi ma da sunan sa ya buɗe.”

Da mujallar Fim ta tambaye ta matakin da za ta ɗauka, sai ta ce “To, ya zan yi da su tunda ban san inda su ke ba? Kawai dai mutane su sani shafin da ake gani a Facebook da suna na, to ba ni ba ce na buɗe, wasu ne su ke yi kuma ba da izini na ba.”
A nata ɓangaren, ita ma Hadiza Aliyu Gabon ta koka da yadda wasu su ke amfani da sunan ta a soshiyal midiya su ke damfarar mutane.
A wani guntun bidiyo da ta yi kuma ta sake shi a shafukan ta, Hadiza ta ja hankalin mutane da su gane sunan da ta ke amfani da shi don guje wa masu damfarar. A cewar ta, “Hadiza Aliyu” shi ne sunan da ta ke amfani da shi a Facebook, a Instagram kuma @adizatou, sannan a TikTok kuma “Hadiza Aliyu Gabon”. Don haka ta ce a riƙa yin taka-tsantsan domin ba za ta roƙi kuɗi ba. “Ba zan ba da ‘account number’ na ba ko kuma in tura maku hannu, don kwanakin baya wani daga Kamaru an kira maman mu aka ce ina buƙatar wani ya turo mini kuɗi. Sai da aka tura mata ‘number: sai ta ce wannan ba na ‘yar ta ba ne.
“Don Allah ba na Facebook!
“Akwai lokacin da aka ce wani ina biza wai ina samar wa mutane su na tafiya Kanada. Ni in kai kai na mana Kanada in da gaske ne ina da aikin da na ke bai wa mutane!
“Ni ma Nijeriyar nan na ke. Ta yaya mutum ya na zaune a Nijeriya kuma a ce ina kai mutum Kanada? Haba, mu riƙa tunani mana. Ni na yi tunani an ce mutum ya na da hankali, kuma yawanci waɗanda ake damfarar nan maza ne, me ya ke damun ku ne? Ba an ce kun fi mu hankali ba?! Haba. Da fatan dai za mu gane. Ni dai ba zan roƙe ku kuɗi ba. Na gode sosai.”
Mujallar Fim ta ruwaito cewa an daɗe ana yin amfani da sunan jarumai a soshiyal midiya da sunan tallata kai ko kasuwanci da kuma damfarar mutane, wadda da dama daga cikin ‘yan fim sun sha fitowa su na ƙaryatawa tare da barazanar shigar da ƙara kotu ga duk wanda su ka samu ya na amfani da sunan su domin cimma wata manufa da su ke da ita.
Ko a wani lokaci a baya sai da Mansurah Isah ta ɗauki matakin gurfanar da wasu matasa a gaban kotu har sai da su ka shafe tsawon mako biyu a gidan yari saboda kama su da kotun ta yi na yin amfani da sunan Iman Sani Danja a Facebook da You Tube domin tallata hajar su.