HAƊAƊƊIYAR Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) ta taya jarumin Kannywood Ali Nuhu murnar naɗin da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi masa a matsayin Manajin-Darakta na Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya (NFC).
Saƙon taya murnar na ƙunshe ne cikin wasiƙar ƙungiyar mai ɗauke da sa hannun shugaban ta Dakta Ahmad Sarari, wadda mujallar Fim ta samu kwafe.
Wasiƙar ta ce, “Mu na taya ka murna game da naɗin da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi maka a matsayin Manajin-Darakta na Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya.
“Mu na matuƙar alfahari da nasarorin da ka samu da su ka zama abin koyi a masana’antar shirya finafinai.
“Mun yi amanna naɗin da aka yi maka zai bunƙasa masana’antar shirya finafinai ta Nijeriya.
“Mu na fatan Allah ya kare ka, ya kuma yi maka jagora wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyan ka.
“Mun yaba da ƙoƙarin ka wajen ciyar da harkar fim gaba a Afirka, musamman masana’antar Kannywood.
“Mu na alfahari da kai bisa nasarorin da ka samu da kuma martabar da ka kawo wa Kannywood.
“Mu na godiya da fahimta, jajircewa, da kuma kasancewar ka abin koyi ga matasan Nijeriya, musamman matasan Arewa da baki ɗayan mu a ƙungiyar MOPPAN.”