• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Friday, June 6, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Mu ‘yan Kannywood ‘ya’yan Ganduje ne, shi ne ya bayar da mu ga Tinubu – Mansurah Isah

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
January 8, 2023
in Labarai
1
Matan APC: Mansurah tare da matan Kannywood mabiya Tinubu a wajen taron yaƙin neman zaɓeMatan APC: Mansurah tare da matan Kannywood mabiya Tinubu a wajen taron yaƙin neman zaɓe

Matan APC: Mansurah tare da matan Kannywood mabiya Tinubu a wajen taron yaƙin neman zaɓe

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

BABBAR furodusa kuma jaruma, Mansurah Isah, ta bayyana cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano shi ne ya ɗauki ‘yan fim na Kannywood ya miƙa su ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, shi ya sa ake ganin kusan dukkan su su na tafiyar jam’iyyar ne.

Furodusar  ta faɗi haka ne a hirar da ta yi da mujallar Fim a Kano.

Masu lura da harkokin masana’antar finafinan sun ga yadda ‘yan fim su ka yi dumu-dumu a cikin harkar siyasa a wannan lokacin, amma a maimakon yadda su ke raba ƙafa a baya sai su ka bayar da ƙarfin su a ɓangare guda. 

Kusan kowane jarumi ko mawaƙi da ya shahara da wuya ka ji ba ya tafiyar jam’iyyar APC, kuma wasu jaruman da a da ba sa shiga harkar siyasa sai a bayan fage, yanzu sun fito tare da su ake tafiya tallar Tinubu.

A ganin wasu masu lura da al’amuran Kannywood, bin ɗan takara ɗaya tilo kamar ragon azanci ne.

Da mujallar Fim ta tambayi Mansurah Isah nata dalilin na yin dumu-dumu cikin harkar siyasa tare da dunƙulewar su ‘yan fim a waje guda, sai ta ce: “To da man ni ina siyasa ana ba ni aikin talla da kuma wasu ayyuka, amma dai ban taɓa shiga harkar na yi yawo ina bikin ɗan takara ba sai a wannan lokacin.

“Kuma ba ni kaɗai ba, mu na da yawa mata da Maza na cikin Kannywood.

“Amma dai a yanzu mun lura da halin da ake ciki, don haka mu ka fito mu nemi ‘yancin mu ta hanyar shiga siyasa da kuma zaɓar ɗan takarar da zai kawo mana cigaba da zaman lafiya a ƙasar mu.”

Mansurah Isah

A kan dalilin su na bin Tinubu, Mansurah ta ce, “A nan Kano kowa ya sani mu ‘yan fim ‘ya’yan Baba Ganduje ne kuma da yake ɗan takarar shugaban ƙasa na APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, mutum ne da ya ke son ‘yan fim, to da ya zo Kano sai Baba Ganduje ya ce, ‘Ga ‘ya’ya na, na ba ka su ka yi tafiya da su don za su yi amfani a yaƙin neman zaɓe.’ Kuma alhamdu lillah an ɗauke mu a matsayin ‘ya’ya duk inda za a je ko a jirgi ko a mota da mu ake zuwa. 

“Don haka duk wani dan fim a Kano ɗan Baba Ganduje ne, don shi baban mu ne kuma masoyin mu ne. Tsakanin mu da shi sai godiya.”

Duk da haka, firodusar ta yi addu’ar Allah ya ba da shugaba ko da ba wanda ‘yan fim ɗin su ke so ba ne in dai shi ne mafi dacewa. Ta ce: “Ina fatan Allah ya ba mu shugabanni nagari a wannan zaɓen da za a yi; ko ba wanda mu ke so ba ne, Allah ya ba mu wanda za mu samu cigaba a ƙasar mu da kwanciyar hankali.”

Loading

Tags: Abdullahi Umar GandujeAPCBola Ahmed TinubuKanoMansurah Isahmatan KannywoodsiyasaZaɓen 2023
Previous Post

Hotuna: Tagwayen Asali sun cika shekara 1 da auren tagwaye

Next Post

Aure: Bilal da Jamila sun zama ɗaya

Related Posts

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN
Labarai

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN

June 3, 2025
MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim
Labarai

MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim

June 2, 2025
Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22
Labarai

Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22

May 20, 2025
Hukuma ta rufe gidajen gala a Kano har sai bayan Ramadan
Labarai

Gwamnatin Kano ta dakatar da haska finafinan Kannywood 22 a intanet da talbijin 

May 19, 2025
Labarai

Gwamnan Kano ya ɗauki nauyin ‘yan Kannywood 5 zuwa Hajjin bana

April 17, 2025
Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu
Labarai

Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu

March 28, 2025
Next Post
Amarya Jamila da angon ta Bilal

Aure: Bilal da Jamila sun zama ɗaya

Comments 1

  1. Abubakar Ibrahim Abaji says:
    2 years ago

    Maulace mansura isa keyi, ta yaya zatayi jam’u bayan akwai yan PDP, PRP, NNPP da dai sauransu. Ta tsaya akan ta da wanda ta sani ba tace duka ba. Mu bamuyi ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!