A JIYA Lahadi, 8 ga Janairu, 2023 mawaƙan nan masu kama da juna kamar an tsaga rama, wato Hassan Sani Abubakar da Hussaini Sani Abubakar, su ka cika shekara ɗaya cur da auren wasu tagwayen kamar su.
Hassan da Hussaini, waɗanda a fagen waƙa ake kira Tagwayen Asali, sun auri Hassana Abdu Bawa da Hussaina Abdu Bawa a gidan Alhaji Bawa Mechanic da ke garin Dutsin-ma, Jihar Katsina, a bara.
Idan kun tuna, mujallar Fim ta kawo labarin cewa a yayin da Hassana ta auri Hassan, Hussaina kuma ta auri Hussaini, a kan sadaki N100,000.
Su ma matan, kamannin su ɗaya kamar an tsaga rama; sai wanda ya san su sosai ne zai iya bambance su.

Lokacin da aka yi auren, Tagwayen Asali sun nuna godiyar su ga Allah a hirar da su ka yi da mujallar Fim, su ka ce: “Wannan rana babbar rana ce a gare mu wadda ba za mu taɓa mantawa da ita ba, kasancewar mun daɗe mu na jiran wannan lokaci, wanda kamar wani abu ne da ka saka a ran ka kuma ka ke tunanin ba zai yiwu ba, cikin ikon Allah, Allah ya tabbatar da shi.”
A jiya, kyawawan ma’auratan da ke zaune a Kano sun wallafa hotunan zagayowar ranar auren su a soshiyal midiya tare da yin rubutu kamar haka: “Alhamdu lillahi it’s exactly 1 year today. May the love we share become stronger as we grow older together. Wishing us a lifetime of happiness. Happy 1st anniversary to us H4_family (TITU & TATU).” Ma’ana, su na murnar cika shekara ɗaya da aure, tare da addu’ar Allah ya ƙaro masu ƙaunar juna a yayin da su ke tare har tsufan su.
Game da ko wasu daga cikin ma’auratan sun samu ƙaruwa kuwa, sai dai mu ce tukuna dai amma ana kan hanya.
Allah ya tabbatar da rabo, amin.

