• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, April 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Mustapha Musty ya ɓara kan masu cewa an daina yayin sa a Kannywood

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
January 29, 2023
in Labarai
0
Mustapha Musty

Mustapha Musty

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

JARUMI a Kannywood, Mustapha Musty, ya ce har yanzu ya na kallon kan sa a matsayin jarumin da ake damawa da shi, don haka lokaci bai tafi da shi ba.

Jarumin ya bayyana haka ne a lokacin tattaunawar sa da mujallar Fim dangane da rashin ganin sa a cikin harkar fim sosai.

Musty ya ce: “Ita harkar fim a yanzu ba kamar a lokacin baya ba ne, saboda a yanzu abubuwa duk sun sauya. Hakan ya sa wasu abubuwa za ka ga kamar babu su, to amma ba wai don babu su ba ne, lokaci ne ya sauya su.

“Yanzu idan ka duba, yanayin kayan aikin da ake amfani da su a baya ba irin na yanzu ba ne. An samu sauyi na kayan aikin waɗanda su ka fi sauƙin sarrafawa, don haka sai aikin ya yi yawa, kowa ma zai iya yi. 

“Kuma a baya ana kai fim kasuwa ne a kasa, to yanzu an wuce wannan lokacin; sai dai ka yi fim ɗin ka ka sayar a gidajen talbijin ko kuma ka saka a soshiyal midiya, a yanzu a nan ake samun kuɗin.”

Da ya juya kan maganar rashin ganin sa kuwa, sai ya ce: “Ai kamar yadda aka samu cigaba a kayan aikin, haka ma a ɓangaren jaruman aka samu sauyi. Saboda an yi yawa, kowa da wajen da ya ke tafiya aiki. 

“Don ka ga ni har yanzu jarumi ne da ake yayi, musamman waɗanda su ke kallon shirin ‘Kwana Casa’in’ ai su na gani na. Kuma ina fitowa a cikin wasu finafinan.

“Amma dai abin da na sani, harkar ce ta bunƙasa, don haka idan ba ka nan ka na can. Hakan ya sa idan mutum ba ya kallon inda ake yin aiki da jarumi sai ya ɗauka kamar ba ya fitowa ne. 

“Ina yi wa jama’ar da su ke tare da ni da har su ke tambaya ta fatan alheri.”

Loading

Tags: jarumaiKwana Casa'inMustapha Mustysauyin yanayitasheyayi
Previous Post

‘Yan sanda sun kama jarumar Kannywood Murja Kunya

Next Post

Abin da ya sa na ke yi wa shugabannin Nijeriya waƙa – Salisu Nuhu Mariri

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
Salisu Nuhu Mariri

Abin da ya sa na ke yi wa shugabannin Nijeriya waƙa - Salisu Nuhu Mariri

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!