TSOHON Shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) na ƙasa kuma fitaccen jarumi, Alhaji Sani Mu’azu (Makama), ya bayyana naɗin Ali Nuhu a matsayin Shugaban Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya da cewa wani sabon zango ne da aka jima ana so a cim masa, wanda zai kawo cigaba ga masana’antar shirya fim a ƙasar baki ɗaya.
Ya ƙara da cewa rashin naɗa wani ɗan Kannywood ya taɓa jagorantar hukumar ya na daga cikin dalilan koma-bayan da industirin ta samu a tsawon shekaru.
Alhaji Sani ya faɗi haka ne a wani saƙon taya murna da ya wallafa a soshiyal midiya jim kaɗan bayan Gwamnatin Tarayya ta bayyana naɗin.
A rubutun, wanda mujallar Fim ta fassaro daga Turanci, shahararren jarumin ya ce: “Kannywood na cike da ɗoki sakamakon naɗa ɗaya daga cikin ‘ya’yan ta da Shugaban Ƙasa Tinubu ya yi a matsayin sabon Manajan-Darakta na Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya.
“Tun da aka kafa Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya, ‘yan Nijeriya da dama sun riƙe ragamar hukumar, daga kan Mista Brendan Shehu zuwa Dakta Hyginus Ekwuazi, Afolabi Adesanya, Dakta Ɗanjuma Dadu har zuwa kan Dakta Chidia Madueke, babu ko ɗaya daga cikin waɗannan da ya zo daga Kannywood. Zai iya yiwuwa wannan na daga cikin dalilan koma-bayan da industirin ta samu.
“Nadin Ali Nuhu alama ce mai nuna sabuwar fatar samun cigaba ga masana’antar baki ɗaya, ba ma Kannywood kaɗai ba, domin, kamar ni ɗin nan, ya na daga cikin ƙalilan ɗin ‘yan wasa da ke aktin a finafinan Arewa da na Kudu.
“Ali Nuhu ya san ƙalubalen da cigaban masana’antar finafinan Nijeriya ke fuskanta baki ɗaya da tsare-tsaren da za a yi a haɓaka ta a irin wannan lokaci da zamanin da mu ke ciki.
“Babu shakka, zai tabbatar da cewa an tafi tare da Kannywood. Kuma abin da Kannywood ke buƙata kenan.
“Ina taya ka murna, Ali Nuhu. Ina taya Kannywood murna.”
Ɗimbin ‘yan Kannywood sun yi caa wajen taya Ali murna.
A cikin su akwai Shugaban MOPPAN na ƙasa, Dakta Ahmad Sarari, wanda jim kaɗan da bayyana naɗin na Ali da sauran mutum 10 a Ma’aikatar Fasaha Da Al’adu ya ce: “Mashaa Allah! Allah ya taya su riƙo. Allah ya sa su kawo cigaba mai amfani a ‘creative sector’ gaba ɗayan ta.
“Mu na taya ɗan mu Ali Nuhu murna ta musamman. Allah ya yi masa jagora.”
Shi ma Shugaban MOPPAN, reshen Jihar Kano, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, ya rubuta cewa, “Ina taya Ali Nuhu murnar samun wannan matsayi.
“Allah ya sa zuwan sa wannan hukuma ya taimaka wa masana’antar mu ta Kannywood ta daɗa samun cigaba. Amin.”
Darakta kuma marubuci Bala Anas Babinlata kuma ya ce naɗin Ali wata babbar dama ce da Kannywood ta samu.
Bala ya ce: “Masha Allah! Gaskiya wannan damar da aka samu fa gagarumar dama ce da Kannywood ba ta taɓa samun dama makamanciyar ta ba.
“Dama ce da idan aka yi amfani da ita yadda ya dace, finafinan Kannywood za su zama international.
“Allah ya yi riƙo da hannun Ali Nuhu wajen yin abin da dace don ciyar da wannan masana’antar gaba.”
Wasu daga cikin ɗimbin ‘yan Kannywood da su ka taya Ali murna sun haɗa da Sani Musa Danja, Saratu Giɗaɗo, Ishaq Sidi Ishaq, Khalid Musa, Rahama Sadau, Abba El-Mustapha, Baballe Hayatu, Adam A. Zango, Momee Gombe, Lawan Ahmad, Hadiza Kabara, Sadiya Yarima, Falalu Ɗorayi, Fati KK, Fauziyya Maikyau, Abdul Amart Mohammed, Aminu Abba Umar (Nomiis Gee), da sauran su da dama.