DUK wata jaruma da ta shigo harkar fim ɗin Hausa, babban burin ta dai shi ne ta samu ta yi suna kuma ta ɗaukaka. Hauwa Mukhtar Tamburawa ta na ɗaya daga cikin jarumai mata da su ka shigo harkar fim domin su samu ɗaukaka wanda hakan ya sa ta shafe tsawon lokaci ta na fafutikar ganin ta cimma burin ta.
A cikin tattaunawar da mujallar Fim ta yi da ita, jarumar ta bayyana irin nasarar da ta ke hange a yanzu a kan ƙoƙarin da ta ke yi na samun cikar burin na ta.
Hauwa ta ce: “To, gaskiya na daɗe a cikin masana’antar Kannywood, don zan iya cewa da kai na fi shekara goma. Sai dai ba wai na mayar da hankali a kan harkar fim ɗin ba; wani lokaci na shigo, wani lokaci kuma na tafi wasu harkokin kasuwancin da na ke yi.
“Amma dai har kullum harkar fim ta na cikin rai na, kuma ina so na yi suna na samu ɗaukaka, don haka ko da na tafi sai ka ga na sake dawowa.”
Da mu ka tambaye ta ko za ta iya tuna finafinan da ta yi tun farkon shigowar ta, sai ta amsa da cewa: “To gaskiya da yake an daɗe kuma a kan saka ni ne fitowa ɗaya ko biyu zuwa uku, to ka ga ba lallai ba ne in iya kawo sunayen su. Amma dai abin ya na rai na kuma ina da burin na ci gaba har na samu na cimma burin da na ke so na kai.”
Ganin ta shafe tsawon lokaci, ko hakan bai sa gwiwar ta ta yi sanyi ba?
Amsa: “To gaskiya ban karaya ba. Zan yi iya ƙoƙari in da zan yi don samun nasarar da na ke nema a cikin harkar fim.”

To ko wanne shirin ta yi? Hauwa Tamburawa ta amsa: “E to, a yanzu ina da burin na zuba kuɗi na yi finafinai na kai na. Bayan wannan kuma a yanzu ina da kyakkyawar alaƙa da masu harkar fim; mun saba da su, don haka duk wani fim idan ya samu wanda ya dace da ni to za a saka ni a ciki.
“Don haka a yanzu ina hangen nasara ta da na ke fatan samu za ta samu nan gaba kaɗan.”
Jarumar ta yi fatan a samu haɗin kai a cikin masana’antar domin, a cewar ta, shi ne zai sa a samu cigaba.