FITACCEN mawaƙin gambara (hip-pop) kuma mai gabatar da shirin nan mai farin jini na ‘Zafafa 10’ da a tashar Arewa 24, Aminu Abba Umar (Nomiis Gee), ya bayyana matsayin sa a kan harkokin siyasa da ake cikin yi a yanzu, ya ce shi siyasar sa ta aƙida ce ba ta kuɗi ba.
Mawaƙin ya faɗi haka ne lokacin da ya ke yi wa mujallar Fim bayani kan dalilin ziyarar da aka gan shi ya kai wa ɗan takarar zama gwamnan Kano a jami’iyyar APC kuma kuma Mataimakin Gwamnan jihar a yanzu, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, kwanan nan.
A hoton shi da Gawuna da ya wallafa a Instagram, mai gabatar da shirin ya bayyana ɗan siyasar da “next Kano State Governor 2023 Insha Allah”, wato “Gwamnan Kano da zai hau a 2023 in Allah ya yarda”, wanda hakan na nuna inda bakin sa ya karkata a yanzu.
A tattaunawar da ya yi da wakilin mu, Nomiss Gee ya bayyana wasu alaƙoƙi da ke tsakanin sa da wasu manyan ‘yan siyasar Kano.
Ya ce: “Kakakin majalisar Jihar Kano, dangin mu ne shi. Shi kan shi Sha’aban Sharaɗa tare mu ka yi karatu da shi. A.A. Zaura kuwa ajin mu ɗaya da shi. Ni ne dai kawai ba na so in yi nan in yi can.
“Amma kuma shi Gawuna tun tuni na ke tare da shi, ba yanzu ba, tun mu na jami’a. In faɗa maka, tun ya na ciyaman na ƙaramar hukuma, kafin ya zama kwamishina.

“Sannan ƙanen sa kuma aboki na ne. Wani lokaci mu kan zauna ‘on a personal level’, mu yi maganar mu. A lokacin da mu ka gama makaranta shekara takwas zuwa goma da su ka gabata, shi ya ɗauki nauyin dukkan abin da mu ka yi da sauran ɗalibai da abokai na.”
Mawaƙin ya ce waɗannan alaƙoƙin sun sanya shi ya kasa gane wanne zai goya wa baya a siyasar.
Ya ce: “Abin ya zama na rasa ina ma zan yi; duk inda na juya sai in ga akwai nawa, hankali duk ya rabu. Kuma da ma can ni ANPP na ke yi, tun a wancan lokacin. Amma ka san yanzu Arewa 24 ka na aiki da kamfani ba za ka iya fitowa ka ce za ka riƙa yin wasu abubuwa ba. Ka san babu ruwan su da maganar siyasa, sai a wannan karon kamar mutum ya na da damar yin talla ko ‘jingle’ ya karɓa, duk da wasu ba iya biyan kuɗin su ke yi ba. Amma kuma ni na yanke a zuciya ta wanda na daɗe ina tare da shi ina mutunci da shi, kuma ‘fan’ ɗi na ne sosai.”
Nomiis Gee ya ci gaba da cewa, “A ranar ma ina kan hanya zan dawo daga Nijar ya kira ni ya ce mani ya na ke, kwana biyu? Na ce masa gani nan zuwa gidan, sai ya ce ai da ma ya na jira na. Kuma ko da na je ba maganar siyasa mu ka yi ba. Hira kawai mu ka yi, ya na tambaya na ina su wane da wane. Kawai daga baya ne ma na ce to wai menene, tunda ina tare da shi bari ma kawai na goya masa baya.
“Amma ina da siyasar da na ke yi. Nan ba da jimawa ba mutane za su gani. Amma ba wai kawai zan zo ina bin wani ba, ko in je can a ba ni wata dubu ɗaya ko wani abu, wannan ba shi ba ne. Ni ina yin abin da zai taimaki al’umma ne.
“Kuma Gawuna mutumin kirki ne, ba shi da matsala, ga shi da hankali, ba za ka taɓa jin shi da wata matsala ba. Kuma shi babu ruwan shi da ka na yin sa ko ba ka yin sa, in ya tashi taimakon ka, taimakon zai yi.
“Wannan hoto da aka gan ni tare da shi ake tambaya abin da ya kai ni wurin sa, ba komai ba ne illa ziyarar sada zumunci.”
Nomiis Gee ya faɗa wa mujallar Fim yadda ‘yan takara daban-daban su ke ta zawarcin sa saboda alaƙar sa da matasan Nijeriya. Ya ce: “Maganar siyasa, ko a satin nan akwai mutanen PDP ‘yan Atiku su na ta kira na, wallahi ba na ɗaukar wayar su! Kai, jam’iyyu da dama su na kira na tun tuni, kowa na so ya kira ni saboda matasa, an san mu ke da matasa, amma ba na son irin wannan siyasar da za ka shiga cikin ruɗu. In ina yin mutum kawai ina yin sa.
“Akwai waɗanda su ka kira ni su ka ce in ba da suna na za su sai mani tikitin jirgi in je Abuja in same su. Ina ganin kamar mutanen Manjo Hamza Al-Mustapha ne. Sai na faɗa masu gaskiya ina ‘busy’!”
![]()






