JARUMA kuma furodusa a Kannywood, Hajiya Ruƙayya Umar Santa (Dawayya), ta ja hankalin matan da ke nuna kwalliyar su ga wasu mazan a soshiyal midiya a maimakon mazajen su na aure.
Don kafa hujja, Dawayya ta ba da labarin wani abu da ya taɓa faruwa da ita a lokacin da ta na gidan mijin ta a cikin wani bidiyo mai tsawon minti biyu da sakan hamsin da ta wallafa a soshiyal midiya.
A bidiyon, wanda mujallar Fim ta rubuto kalaman da Dawayya ta furta a cikin sa, tsohuwar jarumar kuma furodusar ta fara da sallama, sannan ta ci gaba da cewa: “Jama’a barkan mu da warhaka. Kun san me? Wani ɗan taƙaitaccen ‘short story’ na ke so na ba ku, wanda ni a kan kai na ya faru.
“Akwai wata rana lokacin ina da aure, ranar wata Juma’a ba zan manta ba, kafin na yi kwalliya sai maigida na ya ce min an yi wata rasuwa, bari ya je wurin jana’izar nan ya dawo. Sai na ce masa ba matsala.
“So, kafin ya dawo ni kuma sai na yi wanka na yi kwalliya na gyara jiki na, na gyara gida na, na sa turaren wuta, na yi komai a gida na fes-fes.
“Kawai can kafin ya dawo, sai aka yi ‘ringing bell’ ɗin gida na. Ina leƙawa ta kyamara, sai na ga wasu ƙawaye na ne ‘yan Maiduguri, ‘tight friends’ ɗi na ne fa sosai, to amma gaskiya ba su ce min za su zo ba, kuma ni ban ma san sun zo su na Abuja ba.
“Kawai sai na kira maigadin gida na a waya, sai na ce mashi, ‘Waɗannan baƙin me ya sa ka bar su su ka zo?’ Sai ya ce, ‘Ai su su ka ce min kin yi magana da su.’ Sai na ce, ‘A’a, ka zo ka san yadda za ka yi ka gaya masu, don ba su san ina cikin gida ba’.
“Kun san me ya sa na yi haka? Saboda baƙin ciki na miji na na yi wa kwalliya, miji na saboda shi na gyara gida na sa wannan turaren wutan. To, shi na ke so ya fara shigowa ya ji wannan ƙamshin, shi na ke so ya fara ganin wannan kwalliyar tawa, ba na so su su riga shi gani, su ce min na yi kyau. Kun ga dai mata ne ‘yan’uwa na kuma ƙawaye na, amma wallahi ‘sending’ su na yi kuma su ka tafi, sai bayan da ya zo ya ga kwalliyar, ya yaba ya yi komai ya fita tukunna, sai na yi masu waya na ce masu, ‘An ce min kun zo ba na nan’ – kaza-kaza – ‘amma yanzu na dawo’.
“Tukunna sai su ka dawo, mu ka ci gaba da hirar mu ‘normal’ aka yi zumunci.
“So, kun san me ya sa na ba ku wannan tarihin? Matan auren nan na TikTok ku na ke ƙara ja wa kunne, wanda ku burin ku kawai ku sa kaya, ku yi kwalliya ku yi rawar TikTok, ku tallata abin da ku ka yi kwalliya a cikin gidan ku ku tallata shi a duniya ku burge wasu mazan. To sai me?
“Ku kuma mazan da ake yi wa wannan, wallahi matan ku ba su son ku. Duk namijin da ya bar matar sa ta na raye-raye a TikTok, ta na nuna surorin jikin ta a TikTok, wallahi ba ta son shi, kuma shi ma ba ya son ta, kuma ko ƙamshin Aljanna ba za ta ji ba!
“Wallahi tallahi faɗa ne na Manzon Allah, ‘Ka zama dayyuz’ (s.a.w.), ba ka kishin iyalin ka.

“Kuma ke ma da ki ke yi, wallahi ba ki son mijin ki, don duk matar da za ta tsaya ta na tallata surar ta a titi, ki na matar aure, wai kin kwalliya sai kin nuna wa duniya kwalliyar da ki ka yi, kin nuna wa masu mazan, mazan bariki shirme, in da kun ga wasu mazan da ke kallon bidiyon ku, wallahi sai kun yi kuka kun ce me ya sa ma su ka kalle ku!
“Wallahi, wallahi, in kun ga ‘environment’ da irin mutanen da ke da ke ganin wani bidiyon na ku waɗansu mutanen, wallahi sai kun yi nadama. Amma ku gani ku ke kun burge. Wallahi tallahi ba burgewa ba ne.
“Ni dai ina ƙara gaya maku, duk mace da ta ke son mijin ta, ta killace wa mijin ta kan ta ta ke yi, ta ɓoye surorin ta da duk wasu abubuwan ta, mijin ta kaɗai za ta bayyanawa su. Amma ku kun fito ku na bayyana surorin ku a titi, ku na nuna wa mazan duniya, mazan bariki.
“Duk namijin da ya san abin da ya ke in ya kalli bidiyon matar aure sai ya zage ta, saboda shi ma ba zai so tashi matar ta yi ba. Allah ya sa ku gane!”
Ita dai Ruƙayya Dawayya, ta yi aure ne da wani ɗan kasuwa a Abuja mai suna Alhaji Adamu Teku, amma auren ya mutu a cikin 2014 bayan shekara biyu da yin sa. Allah ya albarkaci auren da ɗa ɗaya, Arafat.
Ni dama jahilai na dauki wainnan Matan masu rawa a tik tock
Aurarraki nawa suka mutu saboda wannan shirmen