• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 11, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Na fi son rubutun littafi a kan na onlayin, inji Nafisa Auwal K/Goje

* 'Na sha gwagwarmaya kafin a karɓe ni a matsayin marubuciya'

by MUKHTAR YAKUBU
November 22, 2024
in Labarai
0
Na fi son rubutun littafi a kan na onlayin, inji Nafisa Auwal K/Goje

Nafisa Auwal K/Goje, marubuciyar 'Tauraruwa'

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

NAFISA Auwal Abubakar Ƙaura Goje tana cikin fitattun mata marubuta da ke tashe a yau. A wannan  cikin tattaunawar da ta yi da mujallar Fim, matashiyar marubuciyar ta bayyana yadda ta samu kan ta a cikin harkar rubutu da kuma rubuce-rubucen da ta yi har ta kai ga cikar burin ta.

FIM: Da farko za mu so ki gabatar da kan ki ga masu karatun mu.

NAFISA AUWAL: Assalamu alaikum. Da farko dai suna na Nafisa Auwal Abubakar, haifaffiyar Jihar Kano, Ƙaramar Hukumar Nassarawa, Unguwar Brigade a yankin Ƙaura Goje wanda da shi ake yi mini inkiyar Nafisa Auwal K/Goje. Na yi makarantar addini tun daga matakin shekaru uku a rayuwa har zuwa shekarar 2016 da Allah ya ba ni ikon sauke Alƙur’ani mai girma a makarantar Nana Asma’u Bintu Fodiyo kuma har zuwa yau ina ci gaba da neman ilimin addini. Na yi firamare a K/goje Primary School, na yi sakandare a makarantar ‘yan mata da ke Gama, GGASS Gama Tudu, inda na kammala a shekarar 2014 wanda har zuwa yanzu ban ci gaba da karatu ba sai dai akwai niyya.

Nafisa Auwal Ƙaura Goje

FIM: A wace shekara kika fara rubutu?

NAFISA: Na fara rubutu tun ina matakin aji shida a firamare. Amma a lokacin kasancewar akwai yarinta ba na iya kammala abin da na fara rubutawa, sai dai kawai na samu ‘yan tsofaffin littattafai na na makaranta na rubuta duk abin da ya zo zuciya ta. Sai lokacin da na shiga aji biyu a ƙaramar sakandire na fara rubutun da gaske, don a wannan lokacin ina tsakiyar karance-karance babu kama hannun yaro.

Ba zan iya cewa ga dalilin da ya ja hankali na na yi rubutu ba, sai dai ko na ce yawan karatun littafi da na tashi cikin masu yi ni ma na tasirantu da shi na fara tun ina da ƙarancin shekaru. Hakan ya taka muhimmiyar rawa wajen jan ra’ayi na wajen rubuta tawa basirar.

FIM: Wane littafin kika fara rubutawa?

NAFISA: Littafin da na fara gwada rubutawa littafin yaƙi ne da muka yi da ƙawa ta Aina’u Musa, amma ba mu kammala ba muka watsar. Dukkan labaran da na rubuta a wancan lokacin babu wanda aka buga sai wannan shekarar ta 2024 na samu nasarar buga littafi na mai suna Tauraruwa wanda da shi ne na fara buga littafi. In-sha Allahu kuma ina fatan ci gaba da bugawa.

FIM: Ko kina cikin wata ƙungiya daga cikin ƙungiyoyin marubuta?

NAFISA: Ina ƙarƙashin ƙungiyar marubuta ta ƙasa, wato ANA, sannan ina cikin ƙungiyar HAF.

FIM: A yanzu harkar rubutu ta koma onlayin. Ko kina da sha’awar ci gaba da rubutun littafi?

NAFISA: Gaskiya ne harkar rubutu ta koma onlayin, amma ni har yau ban taɓa rubuta gudan littafi da na saki a onlayin ba. Na dai taɓa farawa na watsar saboda kawai ina ganin tarihin rubutu na ba zai yi dogon zango ba idan na kasance a onlayin kawai na dogara domin dukkan abin da ka ajiye shi a waya wata rana za ka iya rasa shi, shi ya sa kawai na zaɓi salon buga littafi ko da babu yawa.

FIM: Ko kin shiga wata gasar marubuta da kika yi nasara?

NAFISA: Na shiga gasanni sosai, amma cikin shekarar 2024 ɗin nan da muke ciki, saboda kafin nan ba na cikin marubuta don haka ba na samun labaran gasar.

Nafisa: “Harkar rubutu ta ba ni nasarori da ban taɓa mafarkin zan samu ba”

Na yi nasara a gasar Marubuta Group da matakin farko sai kuma gasar Ɗangiwa da na shiga na tsallake matakin farko da na biyu sai na uku da za a bayyana nan da wani lokaci wanda ba a bayyana waye zakara ba.

FIM: Ya kike ganin yadda saƙon marubuta take isa ga masu karatu a wannan lokacin?

NAFISA: Shi isar da saƙo baiwa ce, ba zamani ba ne. Ko a wancan lokacin da ake ganin marubuta na da ƙafar tsayuwa akwai wanda saƙon nasu ba ya isa, kawai dai suna bilinbituwa a cikin marubuta ne, saboda ƙarancin rubuce-rubucen ake bibiyar su, amma yanzu yawaitar marubuta da rubutun ne ya sa ake wa rubutu kallon hadarin kaji. Amma ko a yanzu akwai ɓangaren da kwalliya take biyan kuɗin sabulu

FIM: Wace nasara kika samu a harkar rubutu?

NAFISA: Harkar rubutu ta ba ni nasarori da ban taɓa mafarkin zan samu ba a rayuwa ta, ciki har da ɗaga suna na daga inda nake zuwa inda ban taɓa zuwa ba.

FIM: Wane irin ƙalubale kika samu a harkar rubutu?

NAFISA: Ƙalubale na a harkar rubutu bai wuce irin gwagwarmayar da na sha kafin karɓuwar suna na a matsayin marubuciya ba. ‘Yan’uwa da ƙawaye har dariya suke yi mini saboda kallon abin da nake a matsayin shirme. Akwai yayyu na da har abin tsokana na zama a gare su a lokacin da nake rubutu, idan na ce duk ranar da na tashi hira da ‘yan jarida a kan harkar rubutu na idan an tambaye ni ƙalubale kuwa zan ce hakan sai ya zama sara da sukan tsokane ni da ita. Yayin da nakan ji takaici wani lokacin ni kai na ji nake kamar ba zan taɓa cimma nasara ba. Amma alhamdu lillah sai ga shi na wuce inda ma nake tunani.

FIM: Wace shawara za ki ba marubuta?

NAFISA: Shawarar da zan bai wa marubuta ita ce mu ƙara haɗe kawunan mu, mu ajiye ɓangaranci duk lamarin da aka samu haɗin kai in-sha Allah za a cimma nasarar da ba ta kaɗan ba.

FIM: To, madalla. Mun gode.

NAFISA: Ni ma na gode sosai.

Loading

Tags: marubuciyamarubutaRubutu
Previous Post

Mawaƙi a Kannywood, Auta Waziri zai angwance

Next Post

Kotu ta dakatar da gwamnatin Kano daga yin shari’a da Rarara

Related Posts

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Fitaccen mawaƙin siyasa Muhammadu Buhari ‘Kosan Waka’ ya kwanta dama
Labarai

Fitaccen mawaƙin siyasa Muhammadu Buhari ‘Kosan Waka’ ya kwanta dama

August 2, 2026
Yadda gwajin ƙwayoyin halitta na jini ya kawo ƙarshen auren Adam A. Zango da Maimuna Musa bayan watanni 11
Labarai

Yadda gwajin ƙwayoyin halitta na jini ya kawo ƙarshen auren Adam A. Zango da Maimuna Musa bayan watanni 11

August 1, 2026
Jami’an gwamnati sun yi zama da Kannywood domin fara aiwatar da shirin ba da inshorar lafiya kyauta ga ‘yan fim na Kano
Labarai

Jami’an gwamnati sun yi zama da Kannywood domin fara aiwatar da shirin ba da inshorar lafiya kyauta ga ‘yan fim na Kano

July 15, 2026
Kannywood tana buƙatar farfaɗo da gidajen sinima domin bunƙasa tattalin arzikin ƙirƙira – Sani Mu’azu
Labarai

Kannywood tana buƙatar farfaɗo da gidajen sinima domin bunƙasa tattalin arzikin ƙirƙira – Sani Mu’azu

July 14, 2026
A hira da mujallar Fim, mawaƙi Ado Gwanja ya aiko da saƙo ga masoyan sa daga gadon asibiti
Labarai

A hira da mujallar Fim, mawaƙi Ado Gwanja ya aiko da saƙo ga masoyan sa daga gadon asibiti

July 9, 2026
Next Post
Kotu ta dakatar da gwamnatin Kano daga yin shari’a da Rarara

Kotu ta dakatar da gwamnatin Kano daga yin shari'a da Rarara

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!