• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 1, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Na soma cimma buri na na yin fice a Kannywood – jarumi Bilal Mustapha

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
September 18, 2022
in Taurari
0
Bilal Mustapha

Bilal Mustapha

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

WANI sabon jarumi da ya fara haskawa a Kannywood, Bilal Mustapha, ya bayyana cewa jurewa da ya yi ne ta sa ya tashi a matsayin ɗan rawa a fim zuwa cikakken jarumi mai jan fim.

Bilal ya na ɗaya daga cikin jaruman da ake hasashen za su yi fice a masana’antar finafinan nan da ɗan wani lokaci.

Tauraruwar sa ta fara haske ne a cikin fim ɗin ‘Ina Da Mata’ inda ya fito a matsayin Buba.

A tattaunawar sa da mujallar Fim, Bilal ya bayyana irin gwagwarmayar da ya sha kafin ya samu kan sa a matsayin jarumi mai jan fim. Ya ce: “Tun ina yaro na ke sha’awar fitowa a fim, don haka a lokacin da na gama sakandare sai na ƙudiri niyyar cimma buri na. Sai na shigo harkar fim, ina ta fafutikar ganin na samu shiga.”

Bilal Mustapha: “Ina so in yi aure”

Ya ƙara da cewa: “A lokacin da na shigo, da harkar rawa na fara wadda in za a yi fim za a kira mu mu yi rawa. Kuma a lokacin ma a baya ake saka ni, amma dai ni ban damu ba, na san zuwa gaba zan zama wani abu. 

“Sannan abin da ya ke ƙara mani ƙarfin gwiwa shi ne yadda mutane su ke cewa na iya rawa, kuma zan fi dacewa na fito a matsayin jarumi. To, wannan ya na sawa na ji ƙarfin gwiwa na ci gaba da yi. Don haka da na daure ka ga a yanzu na fara kaiwa ga matakin cimma buri na.

“A yanzu ina a matsayin jarumi wanda ya ke jan fim har guda biyu: na fito a matsayin jarumin ‘Ina Da Mata’ wanda na fito a matsayin Buba, sai kuma fim ɗin ‘Zo Mu Zauna’ da na fito a matsayin Ɗanladi.

“Duk inda na shiga a yanzu za ka ji an kira ni da Buba ko a kira ni da Ɗanladi.”

Jarumin ya ce, “A yanzu burin da na ke da shi a matsayi na na matashi shi ne na yi aure, kuma ina so na samar da wani kasuwancin nawa na kai na bayan harkar fim da zai zama ko da babu harkar fim, to ina da wata harkar da za ta riƙe ni.”

Loading

Tags: 'Ina Da Mata'Bilal MustaphaburijarumiKannywoodrawa
Previous Post

Jarumar Kannywood Fati S.U. Garba ta bayyana shauƙin rabuwa da mahaifiyar ta shekara ɗaya bayan rasuwar ta

Next Post

Dawayya ta shawarci mata masu tallar jikin su a TikTok

Related Posts

Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi
Taurari

Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi

December 25, 2024
Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’
Taurari

Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’

November 25, 2023
Sayyada Raihan Imam Ahmad (Ƙamshi)
Taurari

Fim riga ce ta arziki – Raihan Imam Ƙamshi

November 20, 2023
Saratu Abubakar
Taurari

Yadda ɗaukaka ta sa na ke rufe fuska – Saratu Abubakar

October 1, 2023
Safna Lawan
Taurari

Buri na a Kannywood ya kusa cika, inji Safna Lawan

August 24, 2023
Cewar Fanan Buzuwa: "Ba zan iya auren ɗan fim ba"
Taurari

‘Yan fim kada mu riƙe sana’a ɗaya – Fanan Buzuwa

June 11, 2023
Next Post
Ruƙayya Dawayya a cikin bidiyon nasihar da ta yi wa ma'aurata

Dawayya ta shawarci mata masu tallar jikin su a TikTok

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!