• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, July 30, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ni na fara sa Ali Nuhu a fim, amma ana yaɗa ƙarya a tarihin shi – Sani Muhammad Sani

* Ya ƙaryata masu cewa a 'Abin Sirri Ne' Ali ya fara fim

by ALI KANO
May 8, 2024
in Labarai
0
Ni na fara sa Ali Nuhu a fim, amma ana yaɗa ƙarya a tarihin shi – Sani Muhammad Sani

Sani Muhammad Sani (a hagu) da Ali Nuhu

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

FURODUSA kuma darakta a Kannywood, Malam Sani Muhammad Sani, ya ƙaryata masu cewa ‘Abin Sirri Ne’ fim ɗin Ali Nuhu na farko.

Sani, wanda ya yi fice a Kannywood tun farkon kafa ta, ya yi wannan kalami ne bayan ya karanta wani taƙaitaccen tarihin Ali Nuhu da aka bayar a Facebook.

Sani mazaunin Jos ne a farkon kafa Kannywood, inda ya shirya finafinai da dama har ya fito a wasu daga cikin su a matsayin jarumi, amma daga baya ya koma Kano da zama.

Haka kuma shi ne wakilin mujallar Fim na Jos a tsawon shekaru daga shekarar 1999. Daga baya ya zama wakilin jaridu da su ka haɗa da Leadership, Blueprint, da Nation a jihohin Yobe, Bauchi, da Zamfara a lokuta daban-daban.

A martanin da ya wallafa a Facebook a yau, daraktan ya ce, “Ƙarya ce tsantsa idan Ali Nuhu ko muƙarraban sa su ka ce fim ɗin sa na farko shi ne ‘Abin Sirri Ne’. Idan wani ya ce fim ɗin Ali Nuhu ne na farko a matsayin babban jarumi, babu laifi.

“Idan mutane su ka cimma da yawa a rayuwar su, sai a riƙa canza tarihin su, musamman ma dai a Nijeriya.”

Sani ya ci gaba da cewa, Ali Nuhu “ya fara a fim ɗi na mai suna ‘Jumma’ ne, ba a matsayin jarumi ba, sannan ya yi ”Yancin Ɗan Adam’ na Waziri Zaiyanu, kafin ya shiga wasu finafinan Nollywood, inda ya yi wasu ƙananan rol a Jos kafin ya koma Kano riƙe da sikirif ɗin ‘Abin Sirri Ne’ da ‘Dijengala’ lokacin da wani furodusa ya baƙanta masa rai da aka gabatar masa da waɗannan sikirif ɗin.

“Ali Nuhu ya je Kano da sikirif ɗin biyu ne cikin ɓacin rai lokacin da furodusan ya ƙi shirya fim ɗin saboda duhun launin fatar Ali Nuhu. Ya fi so a sa ɗan wasa mai hasken launin fata ya ja fim ɗin, Ali Nuhu kuma ya dage kan cewa lallai sai ya ja finafinan.”

Sani ya ce, “Ali Nuhu ya taɓa faɗa mani cewa ya ɗauko sunan ‘Abin Sirri Ne’ daga wata magana da na ke yawan furtawa a kai a kai. Ina furta wannan kalamin a kusan kowace magana a lokacin.”

Ya ƙara da cewa, “Abin takaici ne yadda ake gurɓata da lalata tarihin rayuwa a Nijeriya saboda marubuta ba su damu su yi tafiya domin su binciko sahihan bayanai kan mutumin da za su rubuta tarihin sa, ko kuma marubucin ya na so ne ya gamsar da wanda ya ɗauke shi aiki ko kuma wanda ake rubuta tarihin rayuwar sa ɗin ko kuma ya na so ya ɓoye wani abu da zai iya zama abin kunya ko kuma ya yi niyyar hana wasu mutane samun yabo kan nasarar da ya samu.”

A ƙarshe ya ce, “Yawancin tarihin Kannywood ƙarya ne kawai wasu da ake kira furofesoshi da masu son kai, marubuta masu nuna ɓangaranci, marasa ƙwarewa, waɗanda ba su damu da su ƙosar da jama’a da ƙarya a yayin da su ka hakimce cikin ofisoshin su ba.”

Loading

Tags: Abin Sirri NeAli NuhuDijengalaJummaSani Muhammad Sanitarihin KannywoodWaziri Zaiyanu
Previous Post

Gwamnatin Tinubu ba za ta kafa sansanonin soji na ƙasashen waje a Nijeriya ba – Minista

Next Post

Gwamnatin Tarayya ta musanta iƙirarin Binance na neman cin hanci

Related Posts

Wani mai suna Bashir Abdullahi ya damfare ni miliyan bakwai da rabi, inji Halisa
Labarai

Wani mai suna Bashir Abdullahi ya damfare ni miliyan bakwai da rabi, inji Halisa

July 28, 2025
Gaskiyar magana kan ji-ta-ji-tar ‘mutuwar’ Aminu Ala
Labarai

Gaskiyar magana kan ji-ta-ji-tar ‘mutuwar’ Aminu Ala

July 28, 2025
Labarai

KADIFF 2025: Uganda ta fi yawan finafinai a bikin baje-kolin na Kaduna – Israel Kashim Audu

July 25, 2025
Labarai

Karya dokar liƙi: Kotu ta ɗaure G-Fresh da Hamisu Breaker tsawon wata biyar-biyar

July 24, 2025
‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar
Labarai

‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar

July 23, 2025
Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa
Labarai

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa

July 17, 2025
Next Post
Gwamnatin Tarayya ta musanta iƙirarin Binance na neman cin hanci

Gwamnatin Tarayya ta musanta iƙirarin Binance na neman cin hanci

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!