HUKUMAR Tace Finafinai ta Ƙasa (NFVCB) ta ce taron nan wanda ta ce za ta yi da kamfanonin watsa finafinai a intanet da tashoshin talbijin na satalayit, yanzu za a yi shi ne a ranakun Laraba da Alhamis mai zuwa, wato 1 da 2 ga Disamba, 2021.
A cewar ta, taron ya zama wajibi ne saboda ƙasashen duniya su na damuwa kan irin abubuwan da ake ƙirƙira ana yaɗawa a cikin bidiyo da finafinai ta hanyar intanet da tashoshin talbijin na satalayit da yadda su ke shafar al’adu ko kawo illa a cikin al’umma, da kuma matsayin gwamnatoci wajen kawo gyara a cikin su.
Idan kun tuna, a ranar 11 ga Nuwamba, 2021 mujallar Fim ta ba ku labarin cewa hukumar za ta yi wani gagarumin taro don tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma kamfanonin da ke yaɗa irin waɗannan finafinai da bidiyo, waɗanda ake kira kamfanonin yaɗa ‘OTT’.
‘OTT’ (wato ‘over-the-top’) su ne finafinai, waƙoƙi ko shirye-shiryen talbijin da wasu kamfanoni ke tura wa mai buƙata ta hanyar intanet a bisa irin buƙatar sa, kuma zai riƙa biyan kuɗi, wato irin su Netflix, Amazon, Showmax, Africa Magic, YouTube, Iroko TV da ire-iren su da ke Nijeriya.
Labarin ya biyo bayan wani taro da Alhaji Adedayo Thomas ya yi da manema labarai a Legas.

Taken taron da za a yi a wannan makon shi ne, “Al’amuran Dokokin Tace Finafinai na Nijeriya da Tsarin Kawo Gyara Ga Kamfanonin Yaɗa Finafinai da Bidiyo da Masu Ƙirƙirar Shirye-shiryen Kallo,” wato a Turance, “Implications of Nigerian Censorship Laws and Regulatory Framework for OTT Streaming Services and Content Providers”.
A sanarwar da daraktan hukumar mai kula da shiyyar arewa-maso-yamma, Malam Umar G. Fage, ya ba mujallar Fim, an bayyana cewa, “Wannan muhimmin taro zai kuma yi nazari kan babban lamarin nan na samar da kyakkyawan yanayi ga kamfanonin yaɗa shirye-shirye don su haɓaka aikin su.”
Za a yi taron ne a otal ɗin Marriot da ke unguwar GRA, Ikeja, a Legas a ranar Laraba mai zuwa, 1 ga Disamba da kuma washegarin ranardaga ƙarfe 9:00 na safe a kullum.
Sanarwar ta ce babban mai masaukin baƙi a taron shi ne Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, yayin da Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Ƙasa, Alhaji Adedayo Thomas, zai kasance mai masaukin baƙi.