• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Jaruma Maryam Waziri da ɗan ƙwallo Tijjani Babangida sun angwance

by DAGA IRO MAMMAN
November 28, 2021
in Ranar Murna
0
Amarya Maryam Musa Waziri da angon ta Tijjani Babangida su na yi wa juna kallon ƙuda

Amarya Maryam Musa Waziri da angon ta Tijjani Babangida su na yi wa juna kallon ƙuda

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SHEKARANJIYA, 26 ga Nuwamba, 2021, aka ɗaura auren jarumar Kannywood Maryam Musa Waziri da sahibin ta, tsohon fitaccen ɗan ƙwallon ƙafa na ƙungiyar ‘Green Eagles’ ɗin nan Tijjani Babangida.

An ɗaura auren a Kaltungo, Jihar Bauchi.

A ranar Alhamis, Maryam ta wallafa wani bidiyon ta a Instagram a cikin shigar amarci, ta na bayyana farin ciki da sabon yanayin da ta shiga.

Ta kuma yi addu’ar samun kariya daga Ubangiji game da wannan aure da ta yi.

A bidiyon akwai muryoyin mata masu taya ta murna, har da guɗa.

Angon jarumar haifaffen garin Kaduna ne, kuma shekarun sa 48.

Maryam Waziri da Tijjani Babangida

Bayan wasan da ya yi wa Eagles, Tijjani Babangida ya kuma buga wa ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na ƙasar waje wasa, musamnan ma Ajax ta ƙasar Nezalan da Al-Ittihad ta Saudi Arebiya.

Angon yanzu ya yi ritaya daga buga ƙwallo, sai dai ɗan kasuwa ne kuma ejan na harkar ƙwallo.

Tijjani ya taɓa auren wata Balarabiyar ƙasar Tunisiya mai suna Rabah, wadda ƙanwa ce ga matar shahararren ɗan ƙwallon nan Daniel Amokachi. Amma yanzu sun rabu.

Amarya Maryam na taka rawa a bidiyon da ta wallafa a ranar Alhamis

Babu cikakken bayani game da auren Tijjani da Maryam Waziri, amma wata majiya ta shaida wa mujallar Fim cewa amaryar ta tare a gidan mijin ta a Kaduna. 

Ɗimbin masoya sun taya ma’auratan murna a soshiyal midiya.

Mu ma mu na addu’ar Allah ya ba su zaman lafiya da ƙaruwar arziki, amin.

Amarsu ta ango!
Ta zama tasa! Tijjani ya kama hannun amaryar sa
Amarya na taka rawar murna a cikin guntun bidiyon da ta wallafa

Loading

Tags: aurehausa filmsKannywoodMaryam Musa WaziriTijjani Babangida
Previous Post

Ranar 1 ga Disamba za a fara taro kan nuna finafinai da waƙoƙin Nijeriya ta hanyar intanet

Next Post

Za mu taka wa Netflix da ire-iren su burki domin za su iya jawo fitina, cewar Gwamnatin Tarayya

Related Posts

Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji
Ranar Murna

Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji

August 24, 2026
An ɗaura auren mawaƙi Kawu Ɗan Sarki
Ranar Murna

An ɗaura auren mawaƙi Kawu Ɗan Sarki

August 23, 2026
Uwargida na ce ta biya sadakin aure na da amarya ta – darakta Aminu Saira
Ranar Murna

Uwargida na ce ta biya sadakin aure na da amarya ta – darakta Aminu Saira

August 2, 2026
Bikin auren darakta Aminu Saira a Azare ya ja hankalin jama’a
Ranar Murna

Bikin auren darakta Aminu Saira a Azare ya ja hankalin jama’a

July 31, 2026
An taya Aisar, jikar marubuciya Sadiya Garba Yakasai, murnar cika shekaru 5
Ranar Murna

An taya Aisar, jikar marubuciya Sadiya Garba Yakasai, murnar cika shekaru 5

July 15, 2026
Jarumin Kannywood Tijjani Faraga ya aurar da ‘yar sa ta biyu
Ranar Murna

Jarumin Kannywood Tijjani Faraga ya aurar da ‘yar sa ta biyu

July 12, 2026
Next Post
Shugaban NFVCB, Alhaji Adedayo Thomas, ya na gabatar da jawabi a taron

Za mu taka wa Netflix da ire-iren su burki domin za su iya jawo fitina, cewar Gwamnatin Tarayya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!