MATSALAR Kannywood ba ta shugabanci ba ce, ta rashin alƙibla ce, cewar shugaban ƙungiyar jaruman masana’antar shirya finafinan, reshen Jihar Kano, Malam Alhassan Kwalle.
Kwalle, wanda fitaccen jarumi ne, ya bayyana haka ne a hirar da ya yi da mujallar Fim kan dalilin sa na yin murabus daga shugabancin ƙungiyar kwanan nan.
A tsawon lokaci ana zargin sa da ƙin sauka daga karaga tare da ƙin barin a yi zaɓe wani ya canje shi.
Kwalle ya ce yanzu dai ya sauka, kuma ya koma gefe domin gudanar da harkokin sa na ƙashin kan sa.
Dangane da dalilin sa na yin murabus daga shugabancin ƙungiyar, Alhassan Kwalle ya ce, “Abin da ya sa na sauka daga shugabancin ƙungiyar jaruman dai shi ne ita ƙungiya ba ta yiwuwa mutum ɗaya, kuma ba ta yiwuwa ba a san ina za a kai ta ba.
“To, duba da yadda harkar fim ta samu kan ta a baya, sai mu ka zata rashin shugabanci shi ne ya hana wannan masana’anta ta ci gaba, sai ya zama daga ƙarshe ni na tsinci kai na cikin yaƙinin cewar ba rashin shugabancin ne ya hana masana’antar ci gaba ba, wasu daga cikin ‘yan masana’antar su su ka hana ta kaiwa inda ya kamata ta kai.
“Don haka ni dai shugabancin da na yi babu komai a cikin sa sai raba rigima. To sai na ga ko da ba na shugabancin a matsayi na na wanda ya daɗe a masana’antar kuma ana ganin ƙima ta, zan iya shiga na raba rigima, saboda haka ba sai ina shugabancin ba.
“Sannan su ƙungiyoyin wasu gani su ke wata harka ce da za ka rinƙa samun kuɗi da ita ka na canza gida da riga da sauran su. Amma da yawa wasu ba za su iya fahimtar magana ta ba har sai su ma Allah ya jarabce su da shugabancin irin waɗannan mutanen. Amma ko babu komai na gode wa Allah, don babu wani shugaban da ya samu haɗin kan da na samu, kuma idan har za a tsaya a lissafa mutanen da su ka tsaya tsayin daka don ganin wannan harkar ta ci gaba, to za a saka ni a ciki.”
Fitaccen jarumin ya ci gaba da cewa, “A yanzu ni ina ganin ita masana’antar ba ta da wani haɗin kan da za ka zo ka ce ga wata matsala a zo a haɗu a yi maganin ta. Don ina faɗa maka matsalar ba ta shugabanci ba ce. Saboda a wannan masana’antar mu na da tsarin shugabanci ya fi guda goma, kuma kowanne idan ka kalle shi zai kai masana’antar inda ya kamata a kai. Amma wanne goyon baya su ke samu?
“Saboda haka kawai masana’anta da abin da ya fi tasiri kawai menene a hannun ka? Kai wanene kai?
“Abu biyu idan ka na da su zuwa uku, to za ka iya zama mai juya wannan masana’antar. Na farko idan ka na da ɗaukaka. Sai na biyu kuɗi, babu ruwan wasu da tunanin wanne irin kuɗi ne ka shigo da shi cikin harkar fim, sai kawai ka zama mai faɗa a ji. Na uku shi ne wanda ba shi da tasiri sosai, shi ne idan ka na da mutunci kuma ba ka gudun abin hannun su, to za ka iya faɗa musu a wani lokacin su ji, kuma za ka iya faɗa musu a wani lokacin su botsare maka. To wannan darajar, irin waɗannan shugabannin da mu ke da su irin ta ce da su.
“Wannan ya sa ita masana’antar mun kasa tsayawa mu dunƙule mu fuskanci inda mu ka dosa. To a wannan wa ya ke wani maganar shugabanci? Wa za ka kamo ka ɗora? Don wanda ka kamo ɗin ba lallai ne ya yi abin da ya dace ba.”
Kwalle ya ce ya gode wa Allah da ya zama sun yi shugabancin sun gama lafiya.
“Amma dai ina tabbatar maka da cewar matsalar Kannywood ba ta shugabanci ba ce, ta rashin alƙibla ce.”
![]()







