A YAU Lahadi, 25 ga Yuni, 2023 abokan sana’ar marubuci kuma ɗan sanda Alhaji Auwal Garba Ɗanborno sun kaɗu tare da shiga alhini matuƙa sakamakon rasuwar sa da ta faru a yau.
Tun lokacin da labarin rasuwar ya watsu, jama’a su ka fara rubutu a soshiyal midiya, inda wasu ke tambayar ko da gaske ne, wasu kuma na faɗin Allah ya sa ba gaskiya ba ne. A ƙarshe dai aka tabbatar da rasuwar na sa.
Daga nan kuma sai su ka fara yi masa addu’ar Allah ya jiƙan shi da gafara da sauran addu’o’i. Da yawa su na bayyana cewa mutumin kirki ne, kuma mutumin mutane.
Abin da ya ƙara ɗaga hankalin mutane shi ne saƙon sa na ƙarshe a yau a Facebook, awoyi ƙalilan kafin ya rasu, inda ya rubuta cewa, “Ɓarayin rodin da su ka riga mu gidan gaskiya Allah ya gafarta masu.”
Allahu Akbar! Duniya ba matabbata ba. Shi ya gama yi wa wasu addu’ar samun gafara a wurin Allah, ashe shi ma ɗan lokaci ƙalilan ya rage masa.
Auwal ya rasu ne sanadiyyar haɗarin mota da ya ritsa da shi a garin Jogana da ke Ƙaramar Hukumar Gezawa ta Jihar Kano a hanyar sa ta zuwa gonar sa da ke garin Ringim a Jihar Jigawa inda ya saba yin noma a duk shekara.
Haɗarin ya auku sakamakon wata motar jami’an kwastan sun biyo wata mota da ke ɗauke da shinkafa inda hakan ya sa motar da ya ke ciki ta yi taho mu gama da wata mota. A nan take mutane ne uku su ka rasu, har da shi Auwalu Ɗanborno.
Sadik Auwalu Garba Ɗanborno, ɗan marigayin, ya bayyana wa mujallar Fim yadda su ka samu labarin haɗarin, ya ce: “Ɗan’uwan ya kira baban mu ya na tambayar wanne aiki ne zai yi masa. Sai kawai aka ce da shi ku zo nan Asibitin Sir Sunusi, sun yi haɗari. Kuma hakan ta faru ne da misalin ƙarfe 12 na rana. Ta haka ne mu ka samu labarin rasuwar su.”
A game da tafiyar kuwa, ya ce, “Ba da motar sa ya tafi ba yau, motar haya ya hau, ya bar tasa a gida.”
Auwalu Garba Ɗanborno ya rasu ya na da shekaru 47. Ya na da mata biyu da ‘ya’ya goma – bakwai maza, uku mata.

Auwal ya na ɗaya daga cikin fitattun marubutan littattafan Hausa wanda kuma ya yi rubutu a jaridu, sannan a yanzu kuma ya yi fice wajen sharhi kan al’amurra a soshiyal midiya.
An gudanar da jana’izar marigayin da misalin ƙarfe 4:30 na yamma a gidan su da ke unguwar Kurna a Kano, kuma aka binne shi a maƙabartar Kwakwaci bayan filin sama na Malam Aminu Kano.
Jana’izar ta tabbatar da matsayin Auwal a wajen jama’a, domin kuwa wajen ya yi cikar ƙwari, domin kuwa tun daga ƙofar gidan sa har zuwa maƙabartar duk ɗan mutum ne za ka gani.
Soshiyal midiya ta cika da alhinin wannan babban rashi da aka yi. Ga abin da wasu ke cewa:

MUDASSIR ƘASSIM:
Ɗan’uwa na ne shi. Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Allah ya raham Auwal G. Danbarno. Allah ka sada shi da rahamar ka. Allah ka albarkaci bayan sa don alfarmar Manzon Allah (S.A.W).
“Ɗan’uwa na ne. Mun tashi unguwa ɗaya, gida ɗaya, iyayen mu su na zumunci da juna. Tare aka sa mu primary, tare mu ka shiga sakandare. Tarihi na na yarinta ba zai cika ba sai da shi.
“Yau he is no more. Idan tamu ta zo Allah ka sa mu cika da imani.
“Wa inna in-sha Allah bikum lahiquun”.
ZUWAIRA DAUDA KOLO:
“Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un. Auwalu Garba Ɗanbarno ya rasu! Wannan mutuwa ta buge ni ƙwarai.
“Ɗan’uwa marubuci mai barkwanci, sam ba shi da riƙo. Allahu ya karɓi baƙuncin ka, halin ka na gari ya bi ka.
“Allah ya kyauta namu bayan naka.”
MAJE EL-HAJEEJ HOTORO:
“Rai baƙon duniya: Allah ya jiƙan Ɗanborno. Mutum ne mai zafi da ana yin abu zai iya ɗaukar mataki, ko ya ku ke da shi zai iya yi maka raddi ko martani a kan fahimtar sa. Ya na iya yin daidai ya na iya yin kuskure. A yi faɗa da shi a kuma shirya.
“Ba shi da tsoron bayyana ra’ayin sa da kuma fahimtar sa. Sannan ya na da barkwanci da kuma kirki. Da wahala a gayyace shi taro ko wani abu na cigaban marubuta bai halarta ba. Marubuci kuma mai yin sharhi a kan al’amuran yau da kullum. Jagoran filin ‘Lale Kati’ da ya ke yin tsokaci ko hannun ka mai sanda a kan fahimtar sa.
“Masoyin sunna da Ma’aiki sallallahu alaihi wa sallam. Allah ya jiƙan sa ya kuma gafarta masa.”

BASHIR YAHUZA MALUMFASHI:
“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Tare da nauyayyar zuciya na samu labarin rasuwar marubuci, ɗan’uwa mai barkwanci da zumunci, Malam Auwalu Garba Ɗanborno.
“Batun cewa shi mutumin kirki ne, wannan tabbas ne. Ga shi mai tsinkaye da zurfin tunani, musamman a rubuce-rubucen sa mutum zai tabbatar da haka.
“Mu na roƙon Allah ya yi masa rahama, ya tallafa wa zuri’ar sa, amin!
IBRAHIM SHEME:
“Allah ya jiƙan Alhaji Auwal G. Danbarno, amin. Allah ya kyautata makwanci. Allah ya ba iyalai da abokai da sauran masoya haƙurin jure wannan babban rashi, amin.”
FATIMA IBRAHIM GARBA ƊANBORNO:
“RASUWAR ƊAN’UWA AUWALU GARBA ƊANBORNO, wanda na ke yi wa laƙabi da Yaya AG.
“Na taɓa yin rubutu a baya, na ke cewa wani ne ya hana ni ɗora hotuna na a kan duk wani yanar gizo. Ba kowa ba ne wannan sai Auwalu Ɗanborno.
“Tun kafin in yi aure, ba zan manta ba, na ɗora hotuna a Facebook, ya kira ni ya rinƙa yi mini faɗa da nasiha. Ya kawo mini ƙwararan hujjoji a kan illar ɗora hoto a soshiyal midiya. Tun daga wannan ranar ban sake ɗorawa ba.
“Wata rana na gwada sa ka hoto ɗaya, don in ji me zai ce, sai kawai ya yi comment da tsaki. Na yi dariya, na kuma yi saurin gogewa.
“Har gobe har jibi, na haramta wa kai na saka hoto. Haka zalika duk wanda zai ɗora hotuna na na kan bi mutum in roƙe shi a cire.
“Wanda na kasa hanawa shi ne na ranar aure na. Mutane sun yi yawan da ba zan iya kiran su ɗaya bayan ɗaya ina roƙon a cire hotuna na ba. Amma duk wanda ya ke kusa da ni, ya san babu abin da na tsana a duniya kamar ka ɗora hotuna na.
“Wannan horon daga gare shi na fara samu, daga bisani miji na shi ma ya nuna mini idan ina son ɓacin ran sa, to in ɗora hotuna na. Hakan ya sa na kiyaye. Ko a ‘status’ ban damu da ɗora hoto na ba.
“Abu na biyu da ni Fatima zan iya bayar da shaida a kan sa, ya na da ibada, ya na da ibada, ya na da ibada. Ko a kan hanya ake in-sha Allahu, idan aka kira sallah sai ya yi ‘parking’ ya tafi ya yi.
“Ɗazu da safe ya yi ta faɗo mini a rai, na yi ta zancen sa a zuciya ta. Ashe mutuwa zai yi (kuka). Na yi da na sanin hawa onlayin yau. Na kasa daina kukan rasuwar ka.

“Da wannan na ke shaida wa ‘yan’uwa da abokan arziƙi, idan Auwalu Garba ya taɓa ɓata mini, da gangan ko bisa kuskure, na yafe masa duniya da lahira.
“Na sake firgita ainun. Don girmar Allah duk wanda Auwalu ya taɓa yi masa wani kuskure ku yafe masa. Ku yi masa addu’ar dacewa da rabo.
“Haka zalika idan akwai waɗanda ni ma na taɓa yi masu ba daidai ba, su yafe mini. Ko da gangan ko kuma a rashin sani. Domin na ga yadda duniyar yanar gizo ta ɗauka da rasuwar Auwalu. Na tabbata mu ɗin ‘yan’uwan juna ne. Zaman ka lafiya da mutane ya fi rashin sa.”
JAMIL NAFSEEN:
“Na ji mutuwar nan matuƙa! A marubuta da na sani ban taɓa cin karo da mutuwar da ta buge ni irin ta shi ba.
“Allah ya gafarta masa, Ya sa ka huta, Auwal Ɗanborno.”

