A YAU ne daraktan Kannywood Hassan Giggs da matar sa, tsohuwar jaruma Muhibbat Abdulsalam, su ka cika shekaru 15 cur da aure, don haka su ka shiga soshiyal midiya su ka bayyana farin ciki tare da hamdala.
A wani saƙo da ta wallafa a Facebook da Instagram kan wannan muhimmin zango da su ka kawo, Hajiya Muhibbat ta yi godiya ga Allah da ya nuna masu wannan muhimmin zango, inda su ka zauna a matsayin ma’aurata tare da samun ƙaruwar ‘ya’ya.
Cikin zumuɗi, ta ce: “Alhamdu lillah, alhamdu lillah, alhamdu lillah. Ikon Allah ne da kuma addu’ar iyaye. Allah na gode maka. Godiya mara misaltuwa.
“Allah na gode maka da ka ba ni ikon zama da miji na na tsawon wannan shekaru.

“Ya Allah na roƙe ka don darajar Manzon ka Allah ka sa mutuwa ce za ta raba mu. Ya Allah ka yi wa zuri’ar mu albarka.”
Daga nan tsohuwar jarumar wadda a yanzu ‘yar kasuwa ce mai kamfanin ‘Muhibs Ultra Shine Formula’ inda ta ke sayar da kayan gyaran jiki da na gyaran aure, ta miƙa saƙon godiya ga mijin nata saboda mara mata da ya ke yi. A turance ta rubuta cewa: “@hassan_giggs thanks a lot for always supporting me. May Allah reward you with Jannatul Firdausi, amin. 15 years is not a day job.”
Muhibbat ta wallafa hotuna kamar shida na ita da Giggs da ‘ya’yan su waɗanda su ka ɗauka musamman don murnar zagayowar wannan lokaci.
Shi ma Giggs ya wallafa wani hoto da aka ɗauke su tare da jarumai irin su su Hajara Usman da Fati Yola a ranar auren su a soshiyal midiya.

Auren Giggs da Muhibbat, wanda aka ɗaura a ranar 28 ga Yuni, 2008, ya na daga cikin aurarrakin ‘yan fim da ake ba da misali da su na yadda su ka yi shekaru masu yawa su na zaune lafiya ba tare da sun rabu ko kuma an ji kan su ba.
Allah ya albarkaci auren da kyawawan ‘yan mata guda uku.


