ADDUNIYA GIDAN HORO BA DAUWAMA AKE YI BA,
AUWALU GARBA ƊANBORNO ALLAH YA KARƁI ZANKON KA
Jabbaru khaliƙin komai mai ba mu kana yai maimai,
Gare ka ke biɗar komai Allah Ubangijin jarmai,
Yau ga ni ban iya komai,
Na kasa ci da shan komai,
Domin ko nai rashin goga cikin abokanai jarmai,
Mai dariya a yo sannu ba tsallake mu za ai ba.
Sallim Ala Nabiyullah Almahabubu zaɓi na,
Nurul Huda masoyi na Kai ne ka zam madubi na,
Na kwaikwayon ibada ta wacce na ke wa Sarki na,
Madauwami maƙagi na ka yarda ran fitar rai na,
Na cikasa da kalmar nan Kalmar shahada ba wai ba.
Ɗau duniya sijin Baba ba gu na miƙe sawu ba,
Ɗau duniya gidan Kande ba gun zubar saleɓa ba,
Gyara mu’amala baba ba za ka tauye haƙƙi ba,
Ka yi ta taka ɗan Baba ba a raka ka kwanci ba,
Da sahibai da ‘ya’yan ka ba a bisa ku tare ba.
Rabon da nai zubar kuka Hawaye na biyar juna,
Rabon da naj ji ciwon kai Hawaye na rako juna,
Tun lokacin rashin Ummi abar bugun gaba gu na,
Sai fuju’ar masoyi na abin ya ratsa ƙalbi na,
Ɗanborno yanzu shi ke nan babu rabon mu gana ba.
Idan na sad da kayi na ina tsakar tunani na,
Tafakkuri ya hau kai na ina tadabburi kana,
Ga zucci na karakkaina ta saƙa wan da wan kana,
A take sai hawaye na ya gangaro kumatu na,
Nan take na kaɗa kai na na san ba za a fasa ba.
Rana ta ɗauke numfashi wallahi nan na ke tsoro,
Rana ta sarƙe numfashi da na tuna akwai tsoro,
Yau ga shi yanzu mun tashi yau da batu abin tsoro,
Ga ɗan’uwan mu yau ba shi wannan batu akwai horo,
Ya tambayar ƙuburun shi ka sa ba zai yi kashi ba.
Ka ga mutum abokin mu a ko’ina idan za mu,
Da mu da shi a kan gan mu mu na ta zarrafin kan mu,
Mu na raha tsakanin mu mu na ta zolayar kan mu,
Da sa in sa tsakanin mu A yanzu ga shi an gan mu,
Babu ɗayan tsakanin mu har abada ba zai zo ba.
Rashin na Garba Ɗanborno ya zama izzina gu na,
Na rasa rayuka da yawa waɗanda ke kusanci na,
Na yi rashin kakanni na haɗa uba da ummi na,
Na yi rashi na ƙanne na na rasa wassu ‘ya’ya na,
Na rasa yau amini na babu mutuwar da ban ga ba.
Tun tun tuni ka damu na na rayuwa ta duniyya,
Duk matsayin muƙamin ka da ka mace a duniya,
Kai yanzu taka shi kenan za ai biki a duniya,
Babu abu na fasawa kwana uku na ƙirgayya,
A tsaitsaye a kai kan su ba za a sake waige ba.
Sai dai halin da ka aika a duniya na khairiyya,
Shi za ya zauni shaidar ka a kyautata maka niyya,
Shi zai rake ka zangon ka ya kyautata wa sakayya,
Wannan hali da kyan niyya ne sahibin ka kwanciya,
Barzahu sai hali sallah ba za su ma butulci ba.
Da an bi saka an dawo sai ko batu na gadon ka,
Ba mai kula da bayan ka bayan idon ka ban ran ka,
Wasu cikin zuriyyar ka burin su kassa gadon ka,
In da rabo a ‘ya’yan ka su zan yi ma du’a’in ka,
In ba rabo muradin su su fantama rashin baba.
Haka cikin iyalin ka da an yi takaba barka,
An since tarnaƙi sarƙa sai ko batun wani naka,
Da arziki na gadon ka koma cikin gidajen ka,
Sai tariya da wanin ka matar da ke ta kishin ka,
Ga ta a ban wani naka yin haka ba haramun ba.
Mai hankali da tsinkaye me ya kamata kai waye,
Ka nutsu babu tawaye kar kai hali na ‘yan maye,
Ka nutsu babu nanaye ka sa kula da jirwaye,
Maza ka saita sawaye ka hau tafarki kai waye,
Kai tanadin yawan sallah da kyan hali da ba zamba.
Assahibi aminin ka ke zayyana ta halin ka,
Bagobiri sabocin ka Babarbare aminin ka,
Baban Aminu sunan ka Babban Aminu aboka,
Ango na Binta madalla Allah ya san muradin ka,
Ango na Rabi sai dara Darussalami ba wai ba.
Malam Garba ta’aziyya Farin uba na Ɗanborno,
Ina miƙo ta’aziyya domin rashi na Ɗanborno,
Sannu farar uwa sannu Mahaifiya ta Ɗanborno,
Shekara arba’in da huɗu har da wata shida auno,
Yau kwanaki na Ɗanborno a kabari uku bai ba.
Dakta Aminu Alan Waƙa
Sarkin Ɗiyan Gobir