• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, June 7, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Rasuwar Saratu Giɗaɗo babban giɓi ne a Kannywood, inji MOPPAN

* Cewar Sani Mu'azu: Masana'antar fim ta yi babban rashin da ba za a taɓa mantawa da shi ba

by ABBA MUHAMMAD
April 9, 2024
in Labarai
0
Rasuwar Saratu Giɗaɗo babban giɓi ne a Kannywood, inji MOPPAN

Marigayiya Saratu Giɗaɗo (Daso)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ƘUNGIYAR Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) ta bayyana alhini tare da miƙa saƙon ta’aziyyar ta kan rasuwar fitacciyar jarumar Kannywood, Hajiya Saratu Giɗaɗo (Daso).

Saratu ta rasu ne a safiyar yau bayan ta yi sahur ta kwanta, amma ba ta farka ba.

An yi sallar jana’izar ta a fadar Sarkin Kano sannan aka binne ta a maƙabartar Ɗandolo.

A cikin wata sanarwa ga manema labarai da Sakataren Yaɗa Labarai na ƙungiyar, Malam Al-Amin Ciroma, ya sanya wa hannu a Abuja, MOPPAN ta ce: “Cikin tsananin nauyin zuciya da baƙin ciki Kannywood ke jimamin rasuwar ɗaya daga cikin fitattun taurarin ta, Saratu Giɗaɗo, wacce masoyan ta su ka fi sani da Daso.

“Daso, wadda aka haifa a ranar 17 ga Janairu, 1968, a Gombe, ta kasance fitilar hazaƙa da juriya a cikin masana’antar, wadda ta bar alamar da ba za a iya mantawa da ita ba a finafinan Kannywood.

“Tafiyar Daso a duniyar finafinai ta fara ne a Kano, inda ta fara wani gagarumin aiki da ya shafe sama da shekaru ashirin.

“Daso ta shahara saboda yadda ta nuna jarumtaka mai ƙarfi. Daso ta burge masu kallo tare da ƙwaƙƙwaran wasan kwaikwayon ta, ta ci gaba da bijirowa da jan hankalin masu kallo a duk faɗin yankin.

“Fim ɗin ta na farko, wato ‘Linzami Da Wuta’, wanda kamfanin Sarauniya Movies ya shirya a shekarar 2000, ya zama farkon aikin da ta yi fice inda daga nan ta fito a finafinai da dama da su ka haɗa da ‘Nagari’, ‘Gidauniya’, ‘Mashi’, da ‘Sansani’.

“Ta hanyar sadaukarwa da hazaƙa, sunan Daso ya zama gama-gari, inda ta samu yabo sosai saboda ƙwarewar ta da kasancewar ta a kan allon talbijin.

“Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) ta na miƙa ta’aziyyar ta ga ɗaukacin al’ummar Kannywood kan rashin wannan fitacciyar jaruma.

“MOPPAN ta na’am da irin gagarumar gudunmawar da Daso ta bayar ga masana’antar tare da girmama matsayin mai bin diddigi a Kannywood.

“Alhaji Habibu Mohammed Barde, Shugaban MOPPAN na ƙasa, ya bayyana matuƙar kaɗuwa da baƙin ciki game da rasuwar Daso, inda ya yi nuni da giɓin da ta bari wanda ba za a iya maye gurbin sa ba.

“Shi da dukkan ‘yan’uwan sa na Kannywood sun yi baƙin cikin rashin wata abar ƙauna, ya na yi mata addu’a don samun kwanciyar kabari na har abada a Jannatul Firdausi.

“Yayin da mu ke bankwana da Saratu Giɗaɗo, Allah ya sa tunanin ta ya ci gaba da zaburar da ilahirin masu shirya finafinai da ’yan fim, kuma gadon ta ya dauwama a matsayin shaida ga dauwamammen ikon ba da labari a Kannywood da sauran su.”

Shi ma tsohon Shugaban MOPPAN, Alhaji Sani Mu’azu (Makama), ya miƙa saƙon ta’aziyyar sa a madadin Kwamitin Amintattu na MOPPAN kan rasuwar Daso.

Alhaji Sani ya yi ta’aziyyar ne a cikin wani saƙo da ya wallafa a soshiyal midiya kuma ya turo wa mujallar Fim da kwafe jim kaɗan bayan an ba da sanarwar rasuwar jarumar.

Ya ce, “Cikin baƙin ciki da kaɗuwa na haɗa kai da wasu domin sanar da rasuwar ɗaya daga cikin fitattun jaruman Kannywood, Hajiya Saratu Giɗaɗo, wadda masoyan ta a duniya su ka fi sani da Daso.”

Ya ci gaba da cewa, “Mutuwar ta ta zo da kaɗuwa domin ba ta yi rashin lafiya ba ko kaɗan. Ta kwanta ta kwana lafiya a daren jiya kamar yadda ɗan ta na fari ya tabbatar da cewa ta kasa fitowa yau. Ta rasu tana barci. Abin mamaki ne gaskiya, amma mu Musulmi mun san cewa mutuwa ba ta da makawa, kuma ta na iya zuwa a kowane lokaci. Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un!

“Za a iya tunawa da Daso a matsayin ɗaya daga cikin fitattun jaruman da su ka yi fice a Nijeriya waɗanda su ka fassara nau’o’in rawar da su ka taka; a wasan barkwanci, bala’i, takura mana ruwa. Ta kuma iya taka kowane rol da Hausa ko Ingilishi.

“Ana iya kwatanta Daso da Patience Ozokwo – wato Mama Gee ta Nollywood.

“Daso ta shafe aƙalla shekaru 20 a masana’antar finafinai ta Nijeriya. Kuma ni da kai na na yi aiki tare da ita a finafinai da dama. Har ma ta zauna tare da iyali na a Jos yayin da nake ba da umarnin wani fim mai suna ‘Ɗan-Gari’. Ƙwararriya ce ta ban-mamaki a kan aikin ta.

“Daso ta na burge dubban ɗaruruwan jama’a. Sau da yawa gari na tsayawa call ko ya fashe da dariya idan ta bayyana.

“Daso ta yi ƙoƙarin yin tasiri sosai da duniya ta yi imani ta hanyar shiga cikin ayyukan jinƙai, ba da tallafi ga marasa galihu a cikin al’umma daga mafi girman abin da ta samu ko kuma a matsayin mai shiga tsakanin masu ba da gudunmawa da mabuƙata masu amfana.

“A madadin ‘yan’uwa da Kwamitin Amintattu na MOPPAN, ina miƙa ta’aziyya ta ga ‘yan’uwan ta na kusa, da dukkan ƙwararrun ‘yan fim da ke Kano da ɗaukacin masana’antar finafinai a Nijeriya kan wannan babban rashi. Allah (s.w.t.) ya ba mu ƙarfin jure wannan babban rashi.

“Allah ya yi mata rahama, ya saka mata da Aljannatul Firdausi, amin summa amin.”

Loading

Tags: MOPPANrasuwaSani Mu'azuSaratu Gidado Daso
Previous Post

Saratu Giɗaɗo, jarumar Kannywood, ta rasu

Next Post

Tinubu ya yi ta’aziyyar jarumar Kannywood Saratu Giɗaɗo 

Related Posts

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN
Labarai

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN

June 3, 2025
MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim
Labarai

MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim

June 2, 2025
Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22
Labarai

Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22

May 20, 2025
Hukuma ta rufe gidajen gala a Kano har sai bayan Ramadan
Labarai

Gwamnatin Kano ta dakatar da haska finafinan Kannywood 22 a intanet da talbijin 

May 19, 2025
Labarai

Gwamnan Kano ya ɗauki nauyin ‘yan Kannywood 5 zuwa Hajjin bana

April 17, 2025
Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu
Labarai

Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu

March 28, 2025
Next Post
Tinubu ya yi ta’aziyyar jarumar Kannywood Saratu Giɗaɗo 

Tinubu ya yi ta'aziyyar jarumar Kannywood Saratu Giɗaɗo 

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!