A DAREN jiya Litinin, 27 ga Mayu, Allah ya ɗauki ran tsohuwar shararriyar jaruma a Kannywood, Fatima Usman, wadda aka fi sani da Fati Slow.
Kamar yadda mu ka samu labari, Fati Slow ta rasu ne a wani asibiti da ke garin Abasha na ƙasar Chadi da ke da iyaka da ƙasar Sudan.
Jarumar mai kimanin shekara 39 a duniya ta kai ziyara ne garin na Abasha wurin wasu ‘yan’uwan ta.
Abokan sana’ar ta na Kannywood sun yi matuƙar kaɗuwa da samun labarin rasuwar ta.
An yi jana’izar ta a can kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Tsohuwar jaruma Mansurah Isah, wadda ita ce ta fara ba da sanarwar da rasuwar, ta ce ana zaman makoki a gidan su marigayiyar da ke Unguwa Uku a Kano.
Allah ya jiƙan ta, ya sa Aljanna ce makomar ta.