DATTIJO a Kannywood kuma tsohon Shugaban Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Jihar Kano, Alhaji Sa’idu Isah Gwanja, ya yi rashin mahaifiya, wadda kuma ita ce kishiyar mahaifiyar shahararren mawaƙi kuma jarumi Ado Isah Gwanja ce.
Allah ya yi wa Hajiya Binta rasuwa a yau Talata bayan ta karya kumallo ta koma barci, har lokacin tashin barcin ya yi aka ba ba ta tashi ba.
Alhaji Sa’idu Gwanja ya shaida wa mujallar Fim cewa, “Hajiya ta ɗauki tsawon sama da shekara ashirin ta na fama da ciwon suga da hawan jini.”
Ya ƙara da cewa, “Labarin rasuwar ta riske ni ne da misalin ƙarfe 12:38 a lokacin ina shirin zuwa alwala na tafi sallah.”
Dattijuwar, mai kimanin shekara 82, ta rasu ta bar ‘ya’ya biyu, wato shi Alhaji Sa’idu da ƙanwar sa.
Hajiya Binta ta rasu a gidan da ake kira Gidan Kunun Aya wanda ke Layin Ɗanhassan a unguwar Na’ibawa cikin garin Kano.
An yi jana’izar ta a unguwar Fagge, inda can mijin ta da ‘yan’uwan ta su ke.
Allah ya jiƙan ta, amin.
![]()







