WANI fim mai suna ‘Rule No. 1’ shi ne ya lashe gasar Bikin Bajekolin Finafinai na Duniya na Abuja, wato ‘Abuja International Film Festival’, na shekarar 2022.
Kwamitin shirya gasar, wanda jarumin Nollywood ɗin nan Francis Duru ya jagoranta, shi ne ya bayyana haka a daren jiya Juma’a a wajen rufe bikin na 19 da aka yi a Babban Birnin Tarayya.
Taken taron na bana shi ne ‘Matsaloli Da Damarmakin Da Ke Cikin Juyin Tura Finafinai ta Hanyoyin Intanet a Duniya” (“Challenges and Prospects of Digital Streaming Revolution Globally”).
Duru ya ce a cikin sama da finafinai 600 da su ka shiga gasar kuma kwamitin ya kalle su ne aka zaɓo ‘Rule No. 1’ a matsayin wanda ya yi zarra.
A cewar sa, hakan ta faru ne domin fim ɗin ya isar da saƙon kiwon lafiya da tsafta saboda a samar da ƙasa mai lafiya da zaman lumana.
Ya ce: “Fim ɗin da aka ba na biyu shi ne, ‘Dirty Space’, yayin da fim mai suna ‘My Juju’ ya zo na uku.”
Duru ya ƙara da cewa wanda ya zo na ɗayan an ba shi tukwicin kuɗi rabi miliyan (N500,000), aka ba na biyu N300,000, shi kuma na uku aka ba shi N200,000.
A nasa jawabin, wanda ya ƙirƙiro bikin, wato Fidelis Duker, ya yi nuni da cewa nasarar da ‘Rule No. 1’ ya samu ta nuna buƙatar da ke akwai ta jama’a su riƙa kula da kiwon lafiya da tsafta sosai.
Ya ce: “Bayan annobar Korona (COVID-19), ɗaya daga cikin matsalolin farko da mu ka fuskanta ita ce yawancin mutane sun daina kulawa da kiwon lafiya kamar yadda su ke yi a da.
“Idan kun tuna lokacin annobar Korona, sai ka wanke hannayen ka, kuma ka sa takunkumin fuska, amma yanzu kowa ya koma irin rayuwar sa ta da.
“Ainihi manufar wannan aikin ita ce a ga yadda za a yi mutane su koma wa waccan ɗabi’a ta kula da tsafta fiye da yadda mu ke yi a yau.
“Ya kamata mu nuna matsayin kiwon lafiya da tsaftace muhalli.”
Shi ma a nasa jawabin, Manajan Kayan Sayarwa na kamfanin Hypo Nigeria, Mista Akintayo Akinseloyin, cewa ya yi ƙirƙiro da kayan Hypo da tallata su zai taimaka wajen samar da lafiyayyar ƙasa mai kwanciyar lumana.
Akinseloyin ya ce kamfanin sa ya mara wa shirya Bikin Baje-kolin Finafinai na Duniya na Abuja baya saboda a yayata saƙon kiwon lafiya da tsafta a ƙasar nan.
Ya ce: “Ainihin saƙon da aka gina a kan kiwon lafiya da tsafta wani abu ne wanda kowa da kowa ya kamata ya bai wa muhimmanci a rayuwar sa.
“Tsaftataccen muhalli ya na hana yaɗuwar rashin lafiya kuma ya samar da lafiyayyar al’umma da ƙasa mai cimma nasara.”

Mujallar Fim ta ruwaito labarin da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya bayar cewa sauran finafinan da su ka ci gasa a bikin su ne:
* Gasar gwajin fim ta Freetown ga fim ɗin ‘Flatbush’
* Gwarzon Gajeren Fim, ‘Nigeria’ na Smart Edikan
* Cikakken Fim daga Nijeriya, ‘Enough of the Silence’ na Andrew Amenechi
* Gwarzon Jarumi – Sambasa Nzeribe da fim ɗin ‘Enough of the Silence’ – Nijeriya
* Gwarzon Cikakken Fim (na ƙasar waje) – ‘Identical Justice’
* Gwarzon Kiɗan Cikin Fim – cikin ‘Sin City’ – Nijeriya
* Gwarzon Fim na Ɗalibai – ‘Aminata’ (ƙasar Spain) da ‘Once Upon a Perfect Murder’ (Nijeriya)
* Gwarzon Shiri Kan Al’amari, wato ‘documentary’ – ‘Journey of Igbo Civilisation’ – Nijeriya
* Gwarzon Shirin Katun – ‘Larvae Story’ – ƙasar Koriya
* Gwarzon Darakta – Muyiwa Ademola – fim ɗin ‘Sin City’
* Kyautar Zaɓin Masu Kallo – ‘Obsession’ – Nijeriya.
Mujallar Fim ta yi la’akari da cewa duk da yake a cikin arewacin Nijeriya aka yi bikin finafinan tare da ba da kyaututtukan, babu fim ɗin Kannywood ko wani ɗan Kannywood da ya yi wani tasiri a bikin. Hakan ya yi daidai da faɗar masu iya magana da su ka ce, “Mun zo garin ku mun fi ku rawa, to in kun zo garin mu yaya za a yi?”