WATA kotun majistare da ke Babban Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano ta yanke wa tsohuwar jaruma kuma furodusar finafinan Hausa, Sayyada Sadiya Haruna, hukuncin zaman gidan yari na wata shida sakamakon cin zarafin fitaccen jarumi Isah A. Isah da ta yi.
Kotun ba ta ba ta zaɓin biyan tara ba.
Idan kun tuna, mujallar Fim ta ba ku labari a cikin 2019 kan yadda Isah ya maka Sadiya a kotu a kan zargin ta ci masa zarafi a cikin wani gajeren bidiyo da ta wallafa a Instagram inda ta yi amfani da kalamai masu kaushi.
A bidiyon, tsohuwar ta yi iƙirarin cewa Isah ya yi auren mut’a da ita kuma ya sadu da ita ta dubura ba tare da son ran ta ba.
Haka kuma ta kira shi da manemin mata, mai neman maza, da dai sauran munanan kalamai.
Sakamakon haka, ya maka ta a kotu a ranar 16 ga Oktoba, 2019 bisa zargin ɓata suna, abin da ya saɓa wa Sashe na 391 na kundin final kod.

Da ya ke yanke hukunci a yau Litinin, Mai Shari’a Muntari Ɗandago, ya tura Sadiya Haruna gidan waƙafi domin yin zaman watanni shida ba tare da zaɓin tara ba.
Idan ba a manta ba, a ranar 23 ga Agusta, 2021 wata kotun a Kano ta yanke wa Sadiyar hukuncin sanya ta a makarantar Islamiyya mai suna Darul Hadith domin koyon tarbiyya har na tsawon wata bakwai.
Hakan ya biyo bayan ƙarar da Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kai ta saboda yadda ta ke tallar kayan ƙarin kuzarin maza a soshiyal midiya a cikin kalaman batsa, wanda hukumar ta ce hakan aikata baɗala ne.
Comment:thankyou