• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 11, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Samanja mutum ne wanda ba shi da gefe, inji Mutuwa Dole

by DAGA ABBA MUHAMMAD
November 12, 2023
in Labarai
0
Jama'a na addu'a a bakin kabarin Alhaji Usman Baba Pategi (Samanja Mazan Fama)

Jama'a na addu'a a bakin kabarin Alhaji Usman Baba Pategi (Samanja Mazan Fama)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

TSOHON ɗan wasan kwaikwayo kuma ɗaya daga cikin abokan aikin marigayi Alhaji Usman Baba Pategi (Samanja Mazan Fama), Alhaji Haruna Ɗanjuma Usman (Mutuwa Dole), ya nuna alhini da bayyana wanene Samanja a wurin shi.

Da ya ke zantawa da wakilin mujallar Fim bayan an binne marigayin a yau, Mutuwa Dole ya ce, “Abin da zan iya cewa game da wannan bawan Allah wanda Allah ya ɗauki rayuwar sa, Alhaji Usman Baba Pategi, mun kasance tare shekaru ba kaɗan ba, aƙalla shekara talatin da biyar kama arba’in ma. Allah ya sa mu na tare mu na aiki a gidan Rediyon Talbijin Kaduna, daga baya ya zama Rediyo Nijeriya, mu na kuma sashe guda, ɓangaren shirye-shirye.

“Daga nan kuma na kasance ina biyayya a gare shi a matsayin sa na shugaba na, ɓangaren ilmantar da jama’a, ɓangaren wasan kwaikwayo da kuma shirye-shiye.”

Alhaji Haruna Ɗanjuma (Mutuwa Dole)

A game da halayyar marigayin, Alhaji Haruna ya ce, “Alhaji Usman mutum ne da Allah ya yi masa baiwa, kuma kowa nashi ne, ya na kuma da ƙoƙarin ganin cewa ya kyautata wa jama’a. Bayan haka kuma, ba shi da raini ga na ƙasa da shi da waɗanda su ke kafaɗa guda, ya na girmama na gaba, ya na kuma girmama na ƙasa da shi, abin da na ke nufi kenan.

“Sannan kuma, Alhaji Usman Baba Pategi mutum ne wanda Allah ya yi shi mai basira da hazaƙa da ƙoƙari, kasancewar shi marubuci, mai takurawa wajen isar da saƙo don ilmantar da jama’a a kan abin da ya ke faruwa ta hanyar wasan kwaikwayo.”

Tsohon ɗan wasan ya ƙara da cewa, “Alhaji Usman mutum ne wanda ba shi da gefe, kowa nasa ne kamar yadda na faɗa. Ya riƙe mu, mu mun ɗauke shi uba ne, kuma ya yarda da mu uban mu ne. Ko ta fannin wasan kwaikwayo idan ka yi kuskure, zai gyara maka, ba ya kyarar ka, ya kan kira ka ya ce wane da kaza ka yi haka ya fi dacewa, don kai kamar jakada ne. 

“A dunƙule dai ɗan baiwa ne; duk inda ka ɓullo masa tunanin sa me zai yi don ya kwantar wa jama’a da hankali? Me zai yi ya sa jama’a su kasance cikin nishaɗi? Me zai yi ya daidaita tafiyar kowa ya kasance wani bai riƙe da wani? Kada ya zama ka tashi ka yi abin da zai raba ka da ubangijin ka, zai sa ka zama mai imani, mai jin daɗi, mai manta abin da ya dame ka a rayuwar ka da zai sa ka cikin wata halaka ko cutarwa.

“A dunƙule dai, Alhaji Usman mutum ne. Ubangiji ya yi masa rahama, idan tamu ta zo ya sa mu cika da imani.”

Kamar yadda mujallar Fim ta bada labarin rasuwar Samanja a safiyar yau Lahadi, 12 ga Nuwamba, cikin hukuncin Ubangiji an yi jana’izar sa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. 

An yi masa sallah da misalin ƙarfe 10:00 na safe a masallacin Juma’a na Ja’afaru Estate da ke unguwar Kabala Costain, Kaduna. Daga na kuma aka kai shi gidan sa na gaskiya a maƙabartar Tudun Wada da ke Titin Ɓachama, Kaduna.

Ana yi wa marigayi Samanja addu’a a cikin gidan sa

Wasu daga cikin waɗanda su ka halarci jana’izar sun haɗa da Alhaji Haruna Ɗanjuma (Mutuwa Dole), Nura MC Khan, Sagir Baban Kausar, Shafi’u Magaji Usman (Namaigero), Dikko Yakubu, Baba Shantu, iyalai, ‘yan’uwa, ‘yan jaridu, da sauran manyan mutane.

Allah ya jiƙan Samanja da rahama, amin.

Loading

Previous Post

Samanja Mazan Fama ya kwanta dama

Next Post

Gwamnatin Kano ta dakatar da Malam Ali na ‘Kwana Casa’in’ daga fitowa a fim tsawon shekaru

Related Posts

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Fitaccen mawaƙin siyasa Muhammadu Buhari ‘Kosan Waka’ ya kwanta dama
Labarai

Fitaccen mawaƙin siyasa Muhammadu Buhari ‘Kosan Waka’ ya kwanta dama

August 2, 2026
Yadda gwajin ƙwayoyin halitta na jini ya kawo ƙarshen auren Adam A. Zango da Maimuna Musa bayan watanni 11
Labarai

Yadda gwajin ƙwayoyin halitta na jini ya kawo ƙarshen auren Adam A. Zango da Maimuna Musa bayan watanni 11

August 1, 2026
Jami’an gwamnati sun yi zama da Kannywood domin fara aiwatar da shirin ba da inshorar lafiya kyauta ga ‘yan fim na Kano
Labarai

Jami’an gwamnati sun yi zama da Kannywood domin fara aiwatar da shirin ba da inshorar lafiya kyauta ga ‘yan fim na Kano

July 15, 2026
Kannywood tana buƙatar farfaɗo da gidajen sinima domin bunƙasa tattalin arzikin ƙirƙira – Sani Mu’azu
Labarai

Kannywood tana buƙatar farfaɗo da gidajen sinima domin bunƙasa tattalin arzikin ƙirƙira – Sani Mu’azu

July 14, 2026
A hira da mujallar Fim, mawaƙi Ado Gwanja ya aiko da saƙo ga masoyan sa daga gadon asibiti
Labarai

A hira da mujallar Fim, mawaƙi Ado Gwanja ya aiko da saƙo ga masoyan sa daga gadon asibiti

July 9, 2026
Next Post
Abdul Sahir

Gwamnatin Kano ta dakatar da Malam Ali na 'Kwana Casa'in' daga fitowa a fim tsawon shekaru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!