• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, June 30, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Saratu Giɗaɗo ta zama jakadiyar tallafa wa mabuƙata

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
December 31, 2019
in Labarai
0
Saratu Giɗaɗo ɗauke da satifiket ɗin naɗa ta jakadiyar gidauniyar

Saratu Giɗaɗo ɗauke da satifiket ɗin naɗa ta jakadiyar gidauniyar

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
WATA gidauniya mai suna ‘World Wide Initiative for Community Development and Global Healthcare’ ta naɗa fitacciyar jaruma Saratu Giɗaɗo (Daso) a matsayin jakadiyar ta domin cimma buƙatar ta ta bayar da gudunmawa ga mabuƙata a cikin birnin da ƙauyuka.
 
A ranar Talata, … ga Janairu, 2020 ƙungiyar ta gudanar da taron ta na shekara a Kano, inda aka karrama fitattun mutane cikin su kuwa har da ita Saratun.
 
Baya ga karrama Saratu da aka yi, sai aka naɗa ta a matsayin jakadiya domin tare da ita za a riƙa tafiya a matsayin ta na wadda aka san fuskar ta saboda ta riƙa wayar da kan jama’a dangane da ayyukan ƙungiyar.
 
A ƙaton satifiket ɗin naɗin nata da aka ba ta, wadda jagorar gidauniyar, Dakta Baraka Sani, ta rattaba wa hannu, an nuna cewa za ta yi wannan aiki ne a tsawon shekara ɗaya, wato daga ranar 1 ga Janairu zuwa ranar 31 ga Disamba, 2020.
 
Wakilin mujallar Fim ya ji ta bakin Saratu Giɗaɗo dangane da wannan aiki da aka ɗora mata, inda ta bayyana cewa, “An naɗa ni jakadiya ne domin kasancewa ta wadda aka san fuskar ta a duniya, domin haka za mu yi aiki tare da su.
 
“Duk inda za su je, idan ina da lokaci sai mu tafi tare da su domin wayar da kan jama’a, musamman ma dai na ƙauyuka, don ka san irin wannan idan baƙuwar fuska ya je zai yi wa mutanen da ba su san shi ba bayani zai yi wuya su karɓi abin da ya zo masu da shi duk kyaun sa, amma idan sun saba da ganin fuskar mutum, to domin su gan shi ma su tsaya kuma har su saurari abin da zai faɗa.
 
“Amma ni dai matsayi na a ƙungiyar shi ne jakadiya, don haka ina tare da su a wannan matsayin ne.”
 
Ba wannan ba ne karo na farko da wasu ƙungiyoyi ko kamfanoni su ke ɗaukar ‘yan fim ɗin Hausa a matsayin jakadun su domin tallata manufar su ga jama’a.
 

Loading

Previous Post

Waƙoƙin Hausa 10 mafi fice a shekarar 2019

Next Post

Harkar fim a 2020: Afakallahu, Lamaj, Rikadawa da Rahama Sadau sun kawo mafita

Related Posts

Ƙungiyoyin harkar fim, KAFIGAN da MOPPAN, sun yi wa Rahama Sadau ta’aziyyar rasuwar mahaifin ta
Labarai

Ƙungiyoyin harkar fim, KAFIGAN da MOPPAN, sun yi wa Rahama Sadau ta’aziyyar rasuwar mahaifin ta

June 23, 2025
Mahaifin Rahama Sadau mutumin kirki ne da son jama’a, inji Yerima Shettima
Labarai

Mahaifin Rahama Sadau mutumin kirki ne da son jama’a, inji Yerima Shettima

June 22, 2025
Yadda mahaifin mu ya rasu kwana ɗaya bayan ya dawo daga Makkah – Abba, yayan Rahama Sadau
Labarai

Yadda mahaifin mu ya rasu kwana ɗaya bayan ya dawo daga Makkah – Abba, yayan Rahama Sadau

June 22, 2025
Mahaifin Rahama Sadau ya rasu kwana 1 bayan ya dawo daga aikin Hajji
Labarai

Mahaifin Rahama Sadau ya rasu kwana 1 bayan ya dawo daga aikin Hajji

June 22, 2025
Masanin harshe, Korao Hamadou ya gabatar da haruffan rubutun Hausa na asali a taro a Kano
Labarai

Masanin harshe, Korao Hamadou ya gabatar da haruffan rubutun Hausa na asali a taro a Kano

June 20, 2025
Kotu a Kano ta tsare Tsulange, matashin da ke tare titi yana wanka da yin shigar banza
Labarai

Kotu a Kano ta tsare Tsulange, matashin da ke tare titi yana wanka da yin shigar banza

June 20, 2025
Next Post
Afakallahu da Lamaj

Harkar fim a 2020: Afakallahu, Lamaj, Rikadawa da Rahama Sadau sun kawo mafita

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!