• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 8, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Sauyin da na taras a Kannywood bayan mutuwar aure na – Jamila Lasco

by DAGA ABBA MUHAMMAD
August 7, 2021
in Taurari
1
Sauyin da na taras a Kannywood bayan mutuwar aure na – Jamila Lasco
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

JAMILA Usman (Lasco) tsohuwar jaruma ce wadda ta yi rayuwa a industiri tun zamanin su Safiya Musa. Sai dai a wancan lokacin ba ta samu dama yadda ya kamata ba a masana’antar har ta yi aure.

A yanzu dai Jamila Lasco, wadda ke zaune a Kaduna, ta dawo industiri bayan mutuwar auren ta. Kuma burin ta ya fara cika, saboda yanzu ta na ɗaya daga cikin jaruman da tauraruwar su ta fara haskawa.

A hirar musamman da ta yi da wakilin mu a Kaduna, santaleliyar jarumar ta feɗe wa mujallar Fim biri har wutsiya game da rayuwar ta ta Kannywood a da da kuma yanzu.  

FIM: Ki faɗa wa masu karatu tarihin rayuwar ki a taƙaice.

JAMILA LASCO: Assalamu Alaikum. Suna na Jamila Usman, wadda ake kira da Lasco. An haife ni a cikin garin Kaduna, na yi makarantar boko na tun daga firamare har zuwa sakandiri a Kaduna. Bayan na gama sakandiri, sai na yi aure, daga baya kuma Allah ya sa zaman auren ba zai ɗore ba, na fito.

FIM: Ke wace yare ce?

JAMILA LASCO: Asalin mu Fulani ne na Kamaru, amma dai a nan Nijeriya mu ke gaba ɗaya da iyayen mu.

FIM: Ki na jin Fullanci?

JAMILA LASCO: Ina ɗan ji sama-sama; akwai wanda idan aka yi min zan ji in maida, wani kuma sai dai in maida da Hausa.

FIM: A wane lokaci ki ka shigo harkar finafinan Hausa?

JAMILA LASCO: Gaskiya na daɗe, domin tun kafin in yi aure na ɗan taɓa, daga baya kuma na yi aure. Kuma a lokacin shi wanda zai aure ni ba ya son in yi harkar, kuma fim ɗin da na fito a ciki duk ba su fita kasuwa ba.

FIM: A wacce shekara ki ka fara?

JAMILA LASCO: Gaskiya shekarun da dama! (dariya)

Jamila Usman (Lasco)

FIM: Zai iya kaiwa shekara nawa yanzu?

JAMILA LASCO: Gaskiya zai iya kaiwa shekara 17, tun lokacin su jaruma Safiya Musa.

FIM: Ta wace hanya ki ka bi ki ka shiga harkar?

JAMILA LASCO: Lokacin da na shiga mu na mu’amala da su, don ni ban yi wahalar shiga ba ko kuma wahalar bin wasu hanyoyi don shiga fim, saboda mafi yawancin su sun san ni kuma sun san ni wace ce. Wasun su ma sun san iyaye na da ƙanne na.

FIM: Za ki iya tuna fim ɗin da ki ka fara fitowa a ciki?

JAMILA LASCO: Gaskiya fim ɗin da na fara fitowa a ciki bai fita kasuwa ba, kuma na ma manta sunan sa, ka san shekarun da yawa, sai dai waɗanda na yi daga bayan nan.

FIM: A wancan lokacin ki na da ubangida ne?

JAMILA LASCO: Gaskiya ba ni da ubangida.

FIM: Bayan fitowar ki daga gidan miji, ba ki tunanin sake yin wani auren sai ki ka dawo industiri? Sannan wane ƙalubale ki ka samu a gidan ku?

JAMILA LASCO: Shi dai aure lokaci ne. Ko a wancan lokacin ban sa zuwan sa ba, haka yanzu ma idan ya zo ko yau ko gobe a shirye na ke. A gida kuma na fuskanci ƙalubale sosai a wurin mahaifiya ta, don ba ta yarda ba. Sai daga baya, da ɗan bada baki da dai ɗan abubuwa. Ita sai ta gindaya min wasu sharuɗɗa, na yarda, sannan sai ta amince.

FIM: Bayan dawowar ki industiri, da wane fim ki ka fara?

FIM: Bayan na dawo, na fara yi ne da ‘Farin Wata Sha Kallo’ na Adam A. Zango.

FIM: Zuwa yanzu kin fito a finafinai za su kai nawa?

JAMILA LASCO: Gaskiya na fito a finafinai za su kai biyar ko ma fiye da haka. Wasu har yanzu ba su fito ba, su na kan hanya. Ka san yadda masana’antar ta ke, wasu finafinan fitowa ɗaya kawai za ka yi, wasu fitowa biyu, akwai ire-iren su da dama. Wasu kuma ban ma san sunan su ba.

FIM: Da ki ka dawo industiri, ya ki ka ga yanayin masana’antar a da da kuma yanzu?

JAMILA LASCO: Gaskiya akwai bambanci sosai, domin yadda ake tafiyar da al’amuran masana’antar a da da kuma yanzu ba ɗaya ba ne. A da kafin a saka ka a fim sai an duba bajintar ka da kuma yanayin yadda ka ke gudanar da aktin ɗin ka. Amma ba kamar yanzu ba da sai ka na da uwa a gindin murhu, ma’ana da ƙwauri sai gwiwa; wani in ba ka na da wata alaƙa da shi ba ba zai saka a fim ɗin sa ba, kuma ko fim nawa zai yi. Sai kawai idan Allah ya sa ka na da rabo sai ka ga an saka ka ko da kuwa ba wani mutunci ku ke yi ba.

FIM: Waɗanne irin nasarori ki ka samu a harkar?

JAMILA LASCO: Na samu nasarori kuwa, don ni ban ma san ana ganin finafinai na ba. Idan na fita, sai in ji an tare ni ana tambaya na, “Ke ce Jamila Lasco ta cikin fim kaza ko?” Ko kuma “Ai mun gan ki a fostar fim kaza.” Kuma ni gaskiya ba abin da na ke so irin jama’a. Sai abin ya fara ba ni farin ciki. Wannan ba ƙaramin nasara ba ne a gare ni.

FIM: A baya ana yin manyan finafinai, kuma ana samun manyan kuɗaɗe, amma a yanzu masana’antar ta zama ba kamar da ba. Finafinan da ake yi yanzu yawancin su a YouTube ake ɗorawa ko kuma a saida wa gidajen talabijin. Ta yaya ku ke samun na kashewa daga wurin masu shiryawa?

JAMILA LASCO: To, in dai furodusa ya gayyace ka zai ba ka ko yaya ne. Kai kan ka ka san da yanzu da da ba ɗaya ba ne. Ba kuma za ka ce don wane ya ba ka kaza, lallai shi ma wane dole sai ya ba ni kaza ba; ƙarfi ƙarfi ne; ko yatsun mu aka duba, ba ɗaya su ke ba. Za a ba ka kuɗi ba su kai yadda ka ke so ba, amma a haka za ka haƙura. Wani kuma zai ba ka abin da ba ka taɓa tsammani zai ba ka ba. To haka abin ya ke tafiya. Sai dai haƙuri kawai. Da yardar Allah komai zai daidaita.

Jamila Lasco: Ko yau ko gobe aure ya zo, a shirye na ke

FIM: Wanene ubangidan ki a yanzu?

JAMILA LASCO (dariya): Gaskiya ni ba ni da ubangida.

FIM: Ki lissafa mana wasu daga cikin finafinan da ki ka fito?

JAMILA LASCO: Na fito a ‘Farin Wata Sha Kallo’, ‘Baƙar Baƙuwa’, ‘Sarƙa’, da ‘Lukman’. Waɗanda zan iya tunawa kenan, waɗanda na riƙe sunan su.

FIM: Lokacin da Abdul Amart ya saka gasar waƙar da aka yi wa Gwamnan Kogi Yahaya Bello, ke ma kin shiga gasar? Me ki ka samu? Sannan wa ya ɗauki nauyin yi maki bidiyon da ki ka yi?

JAMILA LASCO: Ni na ɗauki nauyin bidiyon da kai na, ba wani ba ne ya yi min. Kuma abin da aka samu sirri ne wannan! (dariya) Amma tabbas an samu abin alheri, ba a cewa komai. 

FIM: Menene babban burin ki game da wannan harka?

JAMILA LASCO: Gaskiya babban buri na in zama furodusa, in riƙa shirya finafinai na kai na.

FIM: Kin fara samun ɗaukaka a Kannywood. A yanzu idan mijin aure ya zo za ki bar fim ɗin ki yi aure?

JAMILA LASCO: Da gudu zan aje fim in yi aure na. Kuma in dai na yi aure, na yi sallama da harkar fim! (dariya)

FIM: Akwai wani ƙalubale da ki ka fuskanta a masana’antar tun da ki ka dawo?

JAMILA LASCO: Gaskiya ban fuskaci ƙalubale ba.

FIM: Wacece ƙawar ki yanzu a Kannywood?

JAMILA LASCO: Gaskiya ina da ƙawaye da dama, amma ba zan faɗi sunan kowa ba saboda duk wadda ba ka kira sunan ta ba ba za ta ji daɗi ba.

FIM: Wanene jarumin ki?

JAMILA LASCO: Gaskiya kowa nawa ne, ba zan iya cewa wane da wane ne jarumai na ba. Ni kowane jarumi nawa ne tunda duk abokan sana’a ne.

FIM: Jarumai mata fa?

JAMILA LASCO: Haka ma matan, duk nawa ne. Dukkan su babu wacce ba ta burge ni.

FIM: Ya maganar Nollywood? Ki na da sha’awar fitowa a finafinan Kudu?

JAMILA LASCO: Gaskiya ba ni da shi. 

FIM: Menene dalili?

JAMILA LASCO: Ni ra’ayi na na nan a Kannywood. Bar ni kawai a nan.

FIM: A baya kin ce ke Bafulatana ce. Ki na da burin yin fim da yaren Fillanci?

JAMILA LASCO: Gaskiya ina da wannan burin idan na samu dama in-sha Allahu.

FIM: Mecece shawarar ki ga Kannywood baki ɗaya?

JAMILA LASCO: Shawara ta ga masana’antar Kannywood, mu zama tsintsiya maɗaurin ki ɗaya. Dukkan wani abu da zai zama na tashin hankali mu guje shi. Sannan mu ci gaba da ƙarfafa wa juna gwiwa don ganin mun kai ga nasara.

Jamila Usman (Lasco): Ni kowane jarumi nawa ne

Loading

Tags: Adam A. Zangohausa filmsJamila LascoKannywood
Previous Post

Afrika ta Yamma na buƙatar irin tsarin sanya ido a zaɓe na INEC — Yakubu

Next Post

‘Yan Kannywood za su yi wa Umma Ali gangamin addu’a ran Lahadi

Related Posts

Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi
Taurari

Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi

December 25, 2024
Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’
Taurari

Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’

November 25, 2023
Sayyada Raihan Imam Ahmad (Ƙamshi)
Taurari

Fim riga ce ta arziki – Raihan Imam Ƙamshi

November 20, 2023
Saratu Abubakar
Taurari

Yadda ɗaukaka ta sa na ke rufe fuska – Saratu Abubakar

October 1, 2023
Safna Lawan
Taurari

Buri na a Kannywood ya kusa cika, inji Safna Lawan

August 24, 2023
Cewar Fanan Buzuwa: "Ba zan iya auren ɗan fim ba"
Taurari

‘Yan fim kada mu riƙe sana’a ɗaya – Fanan Buzuwa

June 11, 2023
Next Post
‘Yan Kannywood za su yi wa Umma Ali gangamin addu’a ran Lahadi

'Yan Kannywood za su yi wa Umma Ali gangamin addu'a ran Lahadi

Comments 1

  1. Usman Ibrahim says:
    4 years ago

    Allah yasa mudace kuma yazaba Mana mafi alheri masu bukatan aure allah yabasu mazajen aure nagari

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!