SHUGABAN Majalisar Malamai ta Jihar Kano da kuma Arewacin Nijeriya, Sheikh Ibrahim Khalil, ya shawarci Babban Sakataren Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, Alhaji Abba El-Mustapha, da ya haɗa hannu da malamai da attajiran Kano don su fahimci hukumar tare da ba ta gudunmawa kamar yadda ake gani a ƙasashen da su ka ci gaba.
Malamin ya faɗi haka ne a lokacin da El-Mustapha ya kai masa ziyarar gabatar da kai tare da ƙarfafa alaƙar aiki a tsakanin su kwanan nan a Kano.
A jawabin nasa, Sheikh Khalil ya taya sabon shugaban murna tare da ba shi shawarar yin aiki tuƙuru don samar wa hukumar cigaba.

Tun da farko a nasa jawabin, El-Mustapha ya jaddada aniyar sa ta haɗa hannu da duk wata hukuma ko ƙungiya da za ta taimaka wa hukumar sa wajen cimma nasarar ayyukan da ta sa a gaba.
Babban sakataren ya ce ya kai ziyarar ne domin ƙulla alaƙar aiki tare da gabatar da kan sa ga malaman a matsayin sa na sabon shugaban Hukumar Tace Finafinai domin su sanya masa albarka.

Idan ba a manta ba, El-Mustapha ya kai makamanciyar wannan ziyarar ga Hukumar Shari’ar Musulunci ta Kano tare da Hukumar Hisba ta Kano, duk don ƙulla alaƙar aiki tare da kawo wa hukumar cigaba.