ƊAYA daga cikin dattawan Kannywood, Malam Khalid Musa, a yau ya karɓi takardar kama aiki a matsayin sabon mai ba gwamnan Jihar Kano shawara kan harkar fim.
Idan kun tuna, mujallar Fim ta ba ku labari a ranar 30 ga Janairu, 2022 cewa Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya naɗa Malam Khalid matsayin mai taimaka masa kan masana’antar Kannywood, kuma ya naɗa fitaccen jarumin barkwanci, Alhaji Mustapha Nabraska, matsayin mai taimaka masa kan farfaganda.
Naɗe-naɗen sun biyo bayan buƙatar da Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (Motion Picture Practitioners Association of Nigeria, MOPPAN) ta yi masa na ya samar da wani jakade tsakanin gwamnatin sa da masana’antar.
Hakan ta faru ne a daren Asabar, 29 ga Janairu lokacin da gwamnan ya rantsar da sababbin shugabannin ƙungiyar na ƙasa tare da shirya masu liyafar cin abincin dare a Gidan Gwamnati.
A daren ne kuma gwamnan ya rantsar da Khalid da Nabraska.
To a yau, 18 ga Fabrairu, Malam Khalid ya karɓi takardar sa ta kama wannan aiki daga hannun Sakataren Gwamnatin jihar, Alhaji Usman Alhaji, a ofishin sa.

A takardar, wadda Babbar Sakatare mai kula da Sashen Harkokin Bincike, Nazari da Siyasa (REPA), Hajiya Hajiya Bilkisu Shehu Maimota, ta rattaba wa hannu a madadin Sakataren Gwamnatin, an sanar da Khalid cewa mai girma gwamna ya amince da naɗin sa a matsayin Babban Mataimaki na Musamman a kan Kannywood daga ranar 8 ga Fabrairu, 2022.
Haka kuma an sanar da shi cewa, “Wannan naɗi da aka yi maka na amintaka da yarda an yi shi ne bisa kyakkyawan nazarin cancantar ka, dacewar ka da nasarorin da ka samu a baya, sadaukarwar ka ga aiki, cikakken sanin makamar aiki, kishin ƙasa, da biyayyar da ka nuna. Ana fatan za ka yi amfani da waɗannan kyawawan halaye wajen tabbatar da samun nasara a ayyukan da aka sanya ka.”
Hajiya Bilkisu ta ƙara da cewa, “A yayin da mu ke hawa mataki na gaba na cigaban jama’a, ina matuƙar fatan za ka tsare gaskiya kuma ka yi aiki kamar yadda gwamnati ta amince za ka yi.
“Ina addu’ar Allah subhanahu wa ta’ala ya ba ka hikima da ƙwazon gudanar da aiki tuƙuru kamar yadda gwamnati ta ke hangen za ka iya.”
Mutane da dama a industiri sun taya Malam Khalid murnar sabon matsayin da ya samu, tare da taya shi addu’ar Allah ya sa ya sauke wannan nauyi lafiya.
Comments 1