ABDULRASHEED Idris, wanda aka fi sani da A.A. Rasheed Kabala, ya na ɗaya daga cikin matasan daraktoci masu tasowa. Ya ɗauki tsawon shekara 17 a Kannywood. A tsawon waɗannan shekarun, babban burin sa shi ne ya zama darakta. Da yake ya na da hazaƙa, kuma ya sa son abin a zuciyar sa, ya jure da duk wani irin wulaƙanci da cin mutunci da aka riƙa yi masa, har sai da burin sa ya cika. A yanzu a cikin matasan daraktoci masu tasowa a Kaduna, idan ka fara ƙirge dole sai ka sako shi a cikin sahu biyar ɗin farko.
A hirar sa da mujallar Fim, Abdulrasheed ya feɗe biri har wutsiya game da aikin ba da umarni da ya ke yi, kamar haka:
FIM: A matsayin ka na matashin darakta mai tasowa, ya ka ke kallon kan ka a nan gaba?
A.A. KABALA: Alhamdu lillah. A gaskiya ina alfahri da aikin ba da umarni, domin duk ayyukan da na iya a masana’antar nan na fi son daraktin. In ba ka manta ba, a wata hira da ku ka taɓa yi da ni na faɗi haka, kuma cikin ƙanƙanen lokaci daga wannan hirar na fara samun ayyuka. Kuma ga shi ina ta samun nasarori, domin mutane su na yaba aiki na sosai. Sannan ina jin daɗin yadda ake girmama ni, kuma ba wai don na fi wasu ba ne.
FIM: Wane darakta ne ya taimake ka har ka kai wannan matsayin?
A.A. KABALA: Magana ta gaskiya duk a cikin daraktoci babu maigida na irin Mustapha M. Shareef. Domin ni a rayuwa ta, duk wanda zan kira maigida shi ne wanda zai ce min in ka yi kaza, kaza zai ba ka ko kuma ka yi kuskure a wuri kaza, ka gyara. To gaskiya Mustapha ya ba ni gudunmawa sosai, shi ya sa na ke girmama shi, na ke yabon shi, kuma na ke masa fatan alheri a kan irin gudunmawa da ya ke ba ni.

FIM: Waɗanne irin ƙalubale ka ke fuskanta, musamman a Kaduna?
A.A. KABALA: Gaskiya daraktocin mu na garin Kaduna ba su taimakon mu. Abin da na ke nufi, ba wai ka ɗauki kuɗi ka ba mutum ko kuma ka yi masa hidima ba, kawai ka koya wa mutum aiki ta yadda zai dogara da kan shi, har shi ma ya raini wasu. In aka yi maka haka shi kan shi wanda ya koya maka aiki har ka koya wa wani, ko ina ya je zai yi alfahari da kai. Gaskiyar al’amari, har ga Allah ba su yi. Wannan abu ya na baƙanta min rai matuƙa.
Yau idan ka duba, maigida Ali Nuhu, ba zai taɓa yin daraktin shi kaɗai ba, sai ka ga akwai darakta ɗaya, biyu har biyu bayan shi. Haka Adam A. Zango da sauran su. Me ya sa namu ba su yi? Gaskiya bai kamata ba, idan ba a yi, su ta yaya aka yi su ka iya? Ni dai ina jan hankalin daraktocin mu, manyan mu, da su yi ƙoƙari su jawo mu a jiki don mu gudu tare, mu tsira tare. Har kullum irin su Ali Nuhu so su ke yi a koya daga wurin su.
FIM: Ya mu’amalar ka da su manyan naku ta ke a yanzu?
A.A. KABALA: E, gaskiya mu na da kyakkyawar mu’amala, kuma ina girmama su a matsayin waɗanda su ka fi ni. Da ma duk wanda ya riga ka, ya zama dole ka girmama shi, har in kai ma ka na so na ƙasa da kai su girmama ka. Ni dai kawai abin da ba na jin daɗi shi ne wannan abu na kowa kan sa ya sani. Amma akwai girmamawa na musamman tsakani na da su, har ga Allah.
FIM: Ban da ba da umarni, akwai wasu ayyuka da ka ke yi a masana’antar?
A.A. KABALA: Bayan daraktin, ina yin ‘production manager’, ina ‘producing’, sannan kuma ina riƙe kyamara. Gaskiya ina da ƙwarewa a kan waɗannan abubuwa da na faɗa maka.
FIM: Ka faɗa mana wasu daga cikin finafinai da waƙoƙi da ka ba da umarni.
A.A. KABALA: Akwai ‘Ranar Masoya’, ‘Kishi Ko Hauka’, ‘Ƙadadara Ta’, wanda yanzu haka mu na kan aikin sa. Sannan na yi aikin waƙoƙi da dama, kama daga na siyasa da na soyayya, amma ba zan iya sanin yawan su ba.
FIM: Menene babban burin ka a kan ba da umarni?
A.A. KABALA: Magana ta gaskiya, abu na farko shi ne in ga na zama ɗaya daga cikin daraktocin da ake ji da su a Kannywood. Abu na biyu, in an ce ga waɗannan da na koya wa aiki ana damawa da su, abu na uku, in ga cewa na ba da umarni a fim da duk inda aka shiga da shi za a yi alfahari da daraktan fim ɗin. Sannan abu na ƙarshe a ce yau na zama darakta kamar Ali Nuhu, Aminu Saira, Adam A. Zango, Falalu A. Ɗorayi da sauran su.
Akwai wata nasara da na samu kuma domin daraktin. A yanzu ni ne kakakin ƙungiyar daraktoci ta Jihar Kaduna. Ka ga wannan ma ai ba ƙaramar nasara ba ce a cikin rayuwa ta.

FIM: Ya maganar iyali?
A.A. KABALA: Alhamdu lillah. Gaskiyar magana, yanzu haka shirin da na ke yi kenan, nan da zuwa shekarar da za mu shiga in Allah yarda ni ma zan shiga daga ciki. A yanzu haka na kusan gama komai, lokacin ɗaurawa akwai na ke jira, da yardar Allah.