WANI gungun ‘yan fim daga masana’antar Kannywood sun kai ziyarar ta’aziyya ga mai martaba Sarkin Lafiya a Jihar Nasarawa, Alhaji Sidi Bege Muhammad, bisa rasuwar ɗan’uwan sa.
Sun je ta’aziyyar ne daga Kano a ƙarƙashin jagorancin furodusa kuma shugaban ƙungiyar ‘Yahaya Bello Network Group’ (YBN) na ƙasa, Abdul Amart Maikwashewa, a fadar sarkin a jiya Laraba, 20 ga Satumba, 2022.
Da ya ke jawabi a gaban sarkin, Abdul Amart ya yi addu’ar Allah ya jiƙan marigayi Safiyanu Bege, wato ɗan’uwa ga sarkin.
Ya ce: “Mun zo fada ne don yi wa sarki ta’aziyyar rashin ɗan’uwan ka, bayan mun samu labari a lokacin da mu ke gudanar da wani aiki a jihar jiya.”
Ya ƙara da cewa, “Mun ji, kuma mun shaida abubuwa da dama na zaman lafiya da zaman tare ya na tafiya a jihar. Mu na addu’ar Allah ya sa mutuwa ta zama hutu a gare shi na har abada. Allah ya ba ku haƙurin jure wannan rashi da imani.”
Mawaƙi Alfazazi Muhammad ya jagoranci yin addu’a ga mamacin da kuma masarautar domin cigaba da samun zaman lafiya da zaman tare a faɗin jihar.

Da ya ke mayar da jawabi, Sarki Sidi Bege Muhammad ya yi godiya da rakiya a ƙarƙashin jagorancin Abdul Amart na ta’aziyyar, da kuma yanayin kawo zaman lafiya a cikin finafinai a ciki da wajen arewacin Nijeriya.
Sarkin ya ci gaba da cewa: “Kafin yanzu, Arewa da al’adun su da ba a san su a midiya ba, ba a san su ba a idon duniya. Amma da zuwan Kannywood da ma’aikatan ta, al’adun mutanen Arewa an san su a faɗin duniya da ladabi na finafinan su.”
Sarkin ya sa wa tawagar albarka.
Waɗansu daga cikin ‘yan tawagar da aka je ta’aziyyar da su su ne Sadiq Sani Sadiq, Ado Gwanja, Hamisu Breaker, Jamila Nagudu, Momee Gombe, Halima Atete, Maryam Yahaya, Teema Yola, Baba Ari, Ɗan’auta, Fati Shu’uma, Fati S.U. Garba, Minal Ahmad da sauran su.
Dukkan su dai jakadun ƙungiyar YBN ne.


![]()







