DARAKTA a Kannywood, Sadiq M. Mafiya, ya yi nuna yadda ya kamata ‘yan siyasa su riƙa yi a tsakanin su na ɗaukar siyasa ba da gaba ba, musamman ga abokai, abokan aiki, ‘yan’uwa da sauran su.
Don kafa misali da hakan, daraktan ya ɗora hoton su shi da abokin sa aikin sa fitaccen darakta Sanusi Oscar 442 a Instagram, a wurin ɗaurin auren mawaƙi Ɗan Musa Gombe a ranar Asabar da ta gabata, kuma kowanne daga cikin su fuskar sa cike ta ke da fara’a.
Sadiq ya yi rubutu a ƙasan hoton, ya ce: “APC, NNPP, PDP, ga shi siyasa ba ta hana mu zumuncin mu ba, kowa da ra’ayin sa.
“Babu jahili kamar wanda ya ɗauki siyasa da gaba. Allah ya sa mu dace.”
Sadiq Mafiya dai ɗan jam’iyyar APC ne, domin kuwa ya na ɗaya daga cikin na hannun daman Abdul Amart. Tare da shi aka yi hidimar Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello a lokacin da ya fito takarar zama shugaban ƙasa.
Shi kuwa Sanusi Oscar 442 ɗan ga-ni-kashe-nin Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso ne.
Wato kenan a yanzu daraktan ɗan jam’iyyar NNPP ne shi, kuma ɗan Kwankwasiyya. Wannan dalilin ya sanya duk inda za ka gan shi, za ka gan shi sanye da jar hula kamar yadda aka san ‘yan Kwankwasiyya su ke yi.