A DAIDAI lokacin da guguwar siyasa ta ke kaɗa masana’antar finafinai ta Kannywood, yadda kowane jarumi ya ke bin layin da ya ke ganin zai ɓulle masa ko dai a ƙungiyance ko a ɗaiɗaiku, ita ma Mansurah Isah ta ɗauki nata layin. A ƙarƙashin gidauniyar ta ta Today’s Life Foundation ta gayyato ‘yar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, wato Missis Mujeedat Folashade Ojo Ahmed Tinubu, zuwa garin Kano, domin tallafa wa mabuƙata da kuma ziyartar waɗansu muhimman wurare.
A ranar Asabar, 13 ga Agusta, 2022 ne tsohuwar jarumar, wadda ‘yar kasuwa ce a yanzu, ta jagoranci wannan zuwan na Mujeedat wadda ta yi kwanaki biyu a Kano.
Bayan kammala ziyarar, mujallar Fim ta tattauna da Mansurah kan wannan ziyara, kamar haka:
FIM: Yaya aka yi ki ka samu kan ki a cikin harkar siyasar wannan lokacin?
MANSURAH ISAH: To, ni da man tun ina makarantar sakandare ina harkokin sana’a saboda na tashi ne a gidan mu iyaye na masu sana’a ne, kuma da yake su masu jajircewa ne a wajen nema shi ya sa su ka koya mana. Don haka ne mu ka tashi da ƙoƙarin neman na kan mu. Saboda haka, na iya sana’o’i da ayyuka da yawa. Don haka tun kafin ma na shiga fim ina da sana’a ta, don haka ko da na shiga fim ban zauna haka ba, har ta kai ga na samar da gidauniyar da na ke tallafa wa mabuƙata. Don haka ni a yaren mu na Yarbanci ana cewa, “Onan kan o woja”, wato ma’ana, idan za ka shiga kasuwa, ba hanya ɗaya ake bi ba. Wannan ya sa ake ganin na tashi ina neman na kai na. Don haka ko a yanzu zan yi fim zan bi ɗan siyasa da kuma harkar gidauniya ta da na ke yi wanda zan taimaka wa jama’a. Don haka duk inda hanyar cin abinci na ya ke a shirye na ke da na bi shi in dai zai kare mini mutunci na.

To a wannan yanayin ne sai mu ka haɗu da Mrs Mujeedat Folashade Ojo Ahmed Tinubu a wajen taron matan APC da aka yi a Abuja, wanda na gabatar mata da gidauniya ta a matsayin ta na mai tallafa wa mabuƙata domin mu haɗa gwiwa da ita yadda za a taimaki mutanen Kano, kuma zan yi amfani da gidauniyar na tallafa wa tafiyar Bola Tinubu da Shettima. To da mu ka haɗu da ita a lokacin sai mu ka shaƙu da ita, wanda a nan ne na saka mata tunanin zuwa na tabbatar mata su na da masoya a Kano kuma ya kamata ta zo su haɗu ta gan su.
To, ka san mutane su na jin tsoron Arewa saboda labarin da su ke ji, amma sai nuna mata yadda ta ke tunani ba haka ya ke ba, wanda ta ce rabon ta da Arewa tun 1985. Don haka sai na ƙarfafa mata zuwa, da haka har na samu ta zo.
FIM: Yaya zuwan ta ya kasance, tun da ke ce ki ka nemi zuwan nata?
MANSURAH: A gaskiya na ji daɗi sosai kuma na yi amfani da mutanen da na sani a gwamnati da ɓangaren tsaro, wanda duk na samu kulawa a gare ta da ta zo, mu ka yi yawo zuwa gidan Sarki da gidan Aminu Ɗantata da gidanjen marayu da wajen mataimakin gwamna wanda a lokacin Gwamna Ganduje ba ya gari. Kuma cikin ikon Allah kafin ta tafi sai gwamna ya dawo, don haka sai ta koma baƙuwar su, komai na kula da ita da masaukin ta ya koma wajen su, mu ka zama masu bi.
To alhamdu lillahi, wannan ziyarar na ji daɗin ta domin na fitar mata da tsoron Arewa, ta nuna ta ji daɗin zuwa Kano, kuma za ta ci gaba da zuwa saboda yadda ta samu Kano ba kamar yadda ta ke samun labari ba. Ko a nan mun samu kyautata alaƙa tsakanin ta da mutanen Kano kuma za ta bayar da labarin Kano da irin karamcin da aka yi mata, domin mun rabu da ita ta na jin daɗi. Kullum a yanzu idan mu ka yi waya da ita ta na nuna jin daɗin ta da irin abin da aka yi mata a Kano.

FIM: Mecece fatar ki game da wannan ziyarar?
MANSURAH: Ni dai fata ta game da wannan, ina fatan Allah ya sa a yi zaɓe lafiya. Kuma Allah ya sa mu samu shugabannin da za su gyara matsalar ƙasar nan daga halin da mu ke ciki na rashin tsaro. Allah ya kawo mana zaman lafiya.
![]()







