SABON Babban Sakataren Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Malam Abba El-Mustapha, ya bayyana cewa zai yi iya bakin ƙoƙarin sa don ganin ya kawo ci-gaba ga masana’antar Kannywood, kuma ya fita kunyar al’ummar Jihar Kano.
Haka kuma ya ce shi babu wani tunanin aikata bi-ta-da-ƙulli a zuciyar sa.
El-Mustapha ya yi waɗannan kalamai ne lokacin da ya ke zantawa da gidan rediyon Liberty Radio da ke Kaduna.
A hirar da ya yi da wakiliyar gidan rediyon, Wasila Isma’il, shugaban ya ce, “Yanzu magana ake na aiki, ta ya za a yi mu yi ‘promoting’ industiri ɗin mu, ta ya za a yi mu yi ‘sanitising’ industiri ɗin mu, ta ya za a yi mu kai industiri ɗin ‘level’ ɗin da sauran ‘counterparts’ ɗin su ka kai nasu? Wannan shi ne kaɗai buri na, babu wani bambanci, babu wani abu na cewar akwai bi-ta-da-ƙulli ni a zuciya ta.”
Da aka tambaye shi makomar ‘yan fim a zamanin mulkin sa, sai ya amsa da cewa, “Tunda har gwamna ya iya ba ni wannan muƙami, ya na da yaƙinin cewa akwai gudunmawa da zan iya bayarwa. Kuma ya yi la’akari da cewa ɗan cikin harkar fim ne ni, wanda akai ta gogayya, kuma ya na daga cikin mutanen da su ka san ni.
“Alhamdu lillahi kujera ta zo, kuma ina yi wa Allah godiya. Kuma in-sha Allahu zan yi iya bakin ƙoƙari na in ga an kai ga gaci, an fita kunyar al’ummar Jihar Kano.”

A wata sabuwa, mujallar Fim ta ruwaito cewa a gobe Litinin, 24 ga Yuli ne sabon babban sakataren zai shiga ofishin sa domin kama aiki.
Hakan ya biyo bayan karɓar takardar tabbatar da shi a matsayin shugaban hukumar da ya yi a ranar Juma’a da ta gabata a ofishin Sakataren Gwamnati, Dakta Baffa Bichi.
A wata sanarwa da ya yaɗa a soshiyal midiya, El-Mustapha ya yi godiya ga dukkan jama’ar da su ka taya shi murna kuma ya gayyaci dukkan masoya da abokan arziki zuwa raka shi ofishin sa domin kama aiki.
Za dai a haɗu ne da misalin ƙarfe 9 na safe a Gidan Ɗan’asabe da ke titin gidan zu, inda daga nan za a rankaya zuwa ofishin Hukumar Tace Finafinai da ke Titin Maiduguri, a cikin ginin gidan talbijin na jihar.
Sai dai El-Mustapha ya ce duk wanda bai samu zuwa ba, to ya taya shi da addu’a.
Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Jihar Kano (MOPPAN) da Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Arewa (AFMAN) sun ce tare da su za a raka El-Mustapha zuwa ofis gobe.
Kakakin reshen MOPPAN na Jihar Kano, Malam Misbahu M. Ahmad, shi ne ya faɗi haka a cikin wata sanarwa inda ya yi kira da dukkan ‘ya’yan ƙungiyoyin da su fito ƙwan su da kwarkwatar su domin shiga cikin kwambar rakiyar.
A cikin wani gajeren bidiyo da ya wallafa a soshiyal midiya, Misbahu ya yi kira ga “‘yan’uwa na wannan masana’anta kafatani, ga waɗanda su ka samu damar halarta, mu na gayyatar waɗannan ƙungiyoyi biyu, Arewa Film Makers reshen Jihar Kano da MOPPAN reshen Jihar Kano, mu na gayyatar ‘ya’yan wannan masana’anta ranar Litinin, ƙarfe 9:00 na safe, wanda za a yi taron gangamin raka shi Abba El-Mustapha ofishin sa da zai shiga ranar Litinin in Allah ya kai mu. Wannan shi ne goron gayyata ga dukkan wanda ya samu hali.”
Tun da fari a saƙon nasa, sai da Misbahu ya gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf saboda muƙamin da ya ba abokin aikin nasu.
Ya ce: “A madadin ƙungiyar MOPPAN reshen Jihar Kano, tare da Arewa Film Makers reshen Jihar Kano, mu na miƙa saƙon godiya ga zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da dama da ya sake ba mu, ya jaddada wannan kujerar ta shugaban Hukumar Tace Finafinai ta jiha, wanda aka ba wa ɗan cikin mu, Abba El-Mustapha, a matsayin shugaban wannan hukuma.
“Mu na godiya ga Allah, mu na godiya ga gwamna, sannan mu na taya shi Abba Na Abba, Allah Ubangiji ya yi riƙo da hannun sa. Allah ya sa ya abin zame wa sana’antar alkhairi, kuma ya gama lafiya.”
![]()







