MARUBUTAN arewacin ƙasar nan sun bayyana halayyar marigayi Sheikh Yusuf Ali da cewa abar koyi ce.
Hakan ya tabbata ne a wani taron haɗin gwiwa na musamman wanda Ƙungiyar Marubuta ta Nijeriya (ANA), reshen Jihar Kano, da Ƙungiyar Gamayyar Marubutan Arewacin Nijeriya, wato ‘Northern Nigerian Writers Summit’ (NNWS), su ka shirya domin tunawa da kuma nuna alhini kan rasuwar fitaccen malamin kuma mawaƙi, Sheikh Dakta Yusuf Ali.
Mujallar Fim ta bada labarin cewa Ustaz Sheikh Yusuf Ali, wanda shi ne Sarkin Malaman Gaya, ya rasu ne a Kano a daren Lahadi, 6 ga Nuwamba, 2023 bayan ya yi fama da rashin lafiya. Shekarun sa 73 a duniya.
A wannan taron, wanda aka gudanar a yau Lahadi a Laburaren Murtala Muhammed da ke Titin Ahmadu Bello a Kano, an yi jawabai kan tarihin shehin da gudunmawar da ya bayar a fannoni da dama na tsawon rayuwar sa.

Tun da farko, babban baƙo mai jawabi, Farfesa Ibrahim Garba Satatima, a maƙalar da ya gabatar mai taken “Sheikh Yusuf Ali: Nagari Na Kowa”, ya yi bita a kan tarihin rayuwar malamin tun tasowar sa da gwagwarmayar da ya sha har zuwa komawar sa ga Allah.
Daga cikin halayen Sheikh Yusuf da Farfesan ya kawo har da haƙurin sa da nuna dattako a dukkan lamurran sa, kamar kyauta da kuɗi ga maƙwafta. Ya ce aikin da ya yi na ƙarshe shi ne aikawa da kyaututtuka da ya saba yi wa maƙwaftan sa. Farfesa Satatima ya ce: “An yi wannan kyautuka da yamma, kuma zuwa dare Allah ya karɓi abin sa.

Wani halin kuma shi ne taimakon matasa. Satatima ya ce, “Tun bayan rasuwar Malam Adamu Na-Ma’aji, ƙungiyar Fityanul Islam da ya ke jagoranta shi ne ya riƙe ta, kuma har Allah ya yi masa rasuwa matasa na ƙungiyar ba su taɓa samun matsala da shi ba; in dai sun je da buƙata zai shige musu gaba ya yi musu jagoranci a wajen kowane mutum da su ke son gani.
“Baya ga haka, daga cikin halayyar sa, ya na taimako ta hanyar malunta. Da an yi maganar malunta a ƙasar Hausa, to Malam ya na bada sirrika da su ke taimaka wa mutane daga cutukan da su ke damun su na sarari da na ɓoye. Don haka wannan abu na malumta da Malam ya yi shuhura da su sun sa ya yi fice wanda bayan shi ba a samu mai irin wannan ba, sai dai Malam Lawan Ƙalarawi.

“Haka nan Malam idan an koma ɓangaren waƙa, nan ma ya yi fice. Don haka shi tunanin sa ya sha bamban da na sauran malamai.”
Shi ma a nasa jawabin, Farfesa Bello Sa’id na Jami’ar Bayero, Kano, ya bayyana Sheikh Yusuf Ali a matsayin mawaƙin da ya yi shaharar da babu kamar sa, domin duk wani fanni na rayuwa yi waƙa a kan sa kamar fannin noma kiwo, soyayya, aure, da kuma addini. Don haka Malam Yusuf Ali gwarzo ne, abin koyi.”

Ita ma Farfesa Aliyah Adamu Ahmad ta Jami’ar Jihar Sokoto ta yi ɗan gajeren jawabi ta onlayin. Ta yaba wa marigayi Yusuf Ali dangane da hikimar sa wajen tsara waƙoƙin da su ka zama abin ajiyewa don tarihi. A cewar ta, Sheikh ya bayar da gudunmawar da za a daɗe ana tunawa da shi.
Shi ma marubuci kuma ɗan jarida Malam Ɗanjuma Katsina ya yi jawabin sa ne ta yanar gizo. Ya ce: “Lallai Sheikh Yusuf Ali ya bayar da gudunmawar sa sosai a fagen aikin jarida, domin shi ne malami na farko da ya riƙa sayen shafuka a jaridu da kuma gidajen rediyo don gabatar da shirin sa na ‘Ilimi Kogi Ne’, wanda hakan ba ƙaramin cigaba ya samar wa kafafen yaɗa labarai da kuma aikin jarida ba.”

Jama’a dama dai sun yi jawabai a kan shehin malamin tare da nuna alhinin rashin sa da aka yi, su ka ce an samu wani babban giɓi mai wuyar cikewa.
Ɗan malamin kuma halifan sa, Sheikh Misbahu Yusuf Ali, ya yi jawabin godiya a madadin ‘yan gidan su baki ɗaya, inda ya bayyana farin cikin su ga ƙungiyoyin marubutan biyu saboda wannan taro da su ka shirya na tunawa da mahaifin su. A cewar sa, hakan ya nuna malamin na kowa ne, ba ‘ya’yan sa da dangin sa kaɗai ba.
Sheikh Misbahu ya ce: “Don haka mu na godiya da wannan karamcin da aka yi mana. Mun gode. Allah ya bar zumunci.”
Wasu daga cikin iyalan marigayin a taron su ne babbar ‘yar da, Sayyada Bilkisu Yusuf Ali, da ƙanwar ta, Malama Amina Yusuf Ali, waɗanda dukkan su marubuta ne.
Taron ya samu halartar ɗimbin malamai da marubuta da manazarta da masoya da kuma iyalin marigayin.
